kungiyar Mata Musulmi Ta Najeriya (Women In Da’awah), reshen Jihar Neja ta fara tantance marayu da za ta tallafa wa a fannin ilimi wajen samar musu gurabe a makarantu daban-daban don su samu ilimi, kamar kowane yaro, musamman na firamare a Minna.
Shugabar kungiyar, Malama Rabi’atu danladi Makun ce ta sanar wa wakilinmu haka yayin wata ganawa a Minna inda ta nuna sun yi nazarin dacewar taimaka wa wadannan rukunin yaran su samu ingantaccen ilimi bisa la’akari da abin da za su kasance a kasar nan gaba.
Shugabar ta ce bayan samun guraben, kungiyar za ta wadata su da kayan karatu gwargwadon abin da ya sawwaka ga kowannensu domin samun kwalliya ta biya kudin sabulu.
kungiyar, wadda ta tun farko ta rarraba wa zawarawa shinkafa da turamen zannuwa domin karamar sallah, bayan an tunatar da su muhimmancin tawakkali ga Allah kan halin da suka samu kansu a ciki.
Malama Rabi’ah ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a tantance su domin koya musu sana’o’in da duk suke sha’awa, bayan sun kammala kuma a ba su jarin da za su dogara da kansu.
kungiyar Mata Musulmi Ta Najeriya za ta kai marayu makaranta
kungiyar Mata Musulmi Ta Najeriya (Women In Da’awah), reshen Jihar Neja ta fara tantance marayu da za ta tallafa wa a fannin ilimi wajen samar…