✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Mata Musulmi ta Afirka ta gudanar da bita ga matasa

kungiyar Mata Musulmi ta Afirka (AMWA) ta yi wa mata da matasa bita ta yini biyu a kan illolin shaye-shaye da hanyoyin sadarwa na intanet…

kungiyar Mata Musulmi ta Afirka (AMWA) ta yi wa mata da matasa bita ta yini biyu a kan illolin shaye-shaye da hanyoyin sadarwa na intanet da kuma yadda ya kamata ’yan mata su yi mu’amala da samari.
Bitar, wacce aka gudanar a Makarantar Koyon Harshen Larabci ta Jihar Kano (SAS) kwanakin baya, ta sami halartar iyaye mata da matasa, maza da mata, a fadin jihar.
Shugabar kungiyar, Malama Halima Shitu ta bayyana wa Aminiya cewa sun shirya bitar ne ganin yadda al’amuran rayuwa suka tabarbare, musamman ma bangaren matasa, shi ya sa ma suka gayyato matasa suka bayar da laccar, saboda lamarin ya fi tasiri, musamman da yake matasan za su ji daga bakin matasa ’yan uwansu. “Masu sauraren laccar da masu bayar da ita duk matasa ne. Mun yi haka ne don idan matasan suka ji abin daga bakin ’yan uwansu matasa, za su fi saurin yarda da abin da ake gaya musu fiye da idan dattijai ne irinmu, wadanda za su yi zaton muna gaya musu abin da yake daidai da zamaninmu na da ne.” Inji ta.
A makalar da ta gabatar mai taken illolin hanyoyin sadarwa ga matasa, Malama Balaraba Uwais ta bayyana cewa kodayake akwai dimbin alfanu da hanyoyin intanet da ‘facebook’ suka kawo wa rayuwar dan Adam, amma sun taimaka wajen lalacewar al’umma. “Akan sami matasa da ke amfani da hanyoyin ta fuskokin da ba su kamata ba. Muna kiran matasa su yi kokarin amfani da wadannan kafafe wajen ci gaban rayuwarsu, kamar abin da ya shafi bincike na ilimi da sauransu.” Inji ta.
Matan da suka halarci taron bitar sun nuna gamsuwarsu game da abin da suka ji daga bakin malamai da dama. Malama Hadiza Sulaiman ta bayyana cewa, “A gaskiya na karu da laccocin, musamman wadda aka yi kan illolin shaye-shaye, wadda za a iya gane idan yaro ya fara shaye-shaye tun farkon lokaci, kafin abu ya yi nisa. Haka kuma da yadda za mu yi, a matsayinmu na iyaye, mu ga ’ya’yanmu ba su shiga harkar shaye-shaye ba, musamman ta hanyar binciken abokan da suke mu’amala da su.” Inji ta.