✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar masu shayi za ta bayyana kanta ga shugabannin kasa

Shugaban kungiyar masu shayi ta kasa, Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya bayyana shirin da shugabannin kungiyar ke yi na fara ziyartar gwamnonin jihohi da manyan sarakuna…

Shugaban kungiyar masu shayi ta kasa, Alhaji Shu’aibu Abubakar, ya bayyana shirin da shugabannin kungiyar ke yi na fara ziyartar gwamnonin jihohi da manyan sarakuna da sauran jami’an tsaron kasar nan domin gabatar da kanta da yin bayanin mananufofi da ayyukanta.
Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, inda kuma ya nuna tuni sun riga sun yi wa kungiyar rijista da sama mata ofis a Kaduna. Haka nan ya ce sun bude ofisoshin rassanta a duk jihohin Arewa da Abuja, sannan suna sa ran budewa a sauran jihohin, ba da jimawa ba.
Ya yi kira ga masu shayi su baiwa shugabannin kungiyar goyan baya da hadin kai domin a sami cigaba mai amfani.