✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar masu sana’ar shayi ta Jihar Filato ta zabi sabon shugaba

daruruwan ’ya’yan kungiyar masu sana’ar shayi da suka fito daga kananan hukumomin Jihar Filato 17, sun gudanar da taron zaben sabon shugaban kungiyar, a garin…

 Malam Ahmed Abubakar daruruwan ’ya’yan kungiyar masu sana’ar shayi da suka fito daga kananan hukumomin Jihar Filato 17, sun gudanar da taron zaben sabon shugaban kungiyar, a garin Jos, babban birnin jihar a makon da ya gabata.
Wanda suka zaba a matsayin sabon shugaban da ya sami kuru’u 94  shi ne Malam Ahmed Abubakar, ya kayar da  abokin takararsa, Malam Shu’aibu Yusuf, wanda ya sami kuru’u 84.
Da yake jawabi bayan kammala zaben, shugaban kungiyar  na kasa, Alhaji Shu’aibu Abubakar  ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da zaben lafiya. “Wannan zabe da muka gudanar, gwajin dafi ne ga sauran kungiyoyi, domin wasu kungiyoyi ba zabe suke yi ba, nadi suke yi. Don haka muna fatar sauran kungiyoyi za su yi koyi da irin wannan zabe da muke gudanarwa. Muna fatar za mu gudanar da irin wannan zabe a dukkan jihohin kasar nan”. Inji shi.
Ya yi kira ga wadanda aka zaba kan su rike wannan amana da aka damka musu, domin shugabanci wani gagarumin aiki ne, don haka dole ne wadanda aka zaba su tashi tsaye wajen ganin sun kare wannan sana’a da sauran masu gudanar da ita.
Daga nan ya yi  kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomin kan su tallafa wa masu wannan sana’a ta shayi, saboda irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.
Ya ce tun da aka kafa wannan kungiyar gwamnati ba ta tallafa mata ba. Mu ma  muna bukatar a tallafa mana domin wannan sana’a ce ta talakawa kuma muna da dubban mutane a  kowane lungu da sako na kasar nan.
A nasa jawabin, sabon shugaban kungiyar na jihar ta Filato, Malam Ahmed Abubakar ya bayyana farin cikinsa kan yadda ’yan kungiyar suka zabe shi. Sannan sai ya roki Allah Ya ba su ikon yin adalci kan wannan nauyi da aka dora musu. “Za mu dora ayyukanmu kan ayyukan da shugabannin baya suka gudanar, kuma za mu tashi tsaye wajen hada kan ’ya’yan  wannan kungiya da ke Jihar Filato”.  Inji shi.