✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar masu motocin sufuri sun yi sabon Shugaban ruko

Kungiyar masu motocin sufirin ta kasa ta RTEAN tayi sabon shugaban ruko wato Alhaji Musa Maitakobi Shugabanta na Legas. Mambobin majalisar zartawar kungiyar ta kasa…

Kungiyar masu motocin sufirin ta kasa ta RTEAN tayi sabon shugaban ruko wato Alhaji Musa Maitakobi Shugabanta na Legas.

Mambobin majalisar zartawar kungiyar ta kasa wadanda suka yi taro a ranar Talatar da ta gabata a birnin Legas sun shaida wa ‘yan jaridu cewa, sun dakatar da tsohon shugaban Kungiyar Mista Osakpanwan Eriyo, wanda suka ce ya dare bisa kujerar madafun ikon kungiyar ba bisa ka’ida ba kana ya kauce wa tsarin dokar kungiyar inda yake barazana da zaman lafiyar ta da na mambobinta a jihohin daban-daban na fadin kasar nan inda bayan sun rattaba hannun dakatar da shi suka kuma kore shi daga kungiyar nan take suka maye gurbin sa da Alhaji Musa Maitakobi a matsayin ta na ruko yayin da suka maye gurbin babban magatakardar kungiyar Mista Ibrahim Yusuf da Mista Henry Ejiofor bayan shima sun kore shi bisa dalilan biye wa tsohon shugaban kungiyar wajen cin amanar ta.

Da yake wa manema labarai karin haske Alhaji Adamu Zaharaddin mataimakin sakataren kungiyar na biyu wanda ya yi magana da yawun majalisar zartarwa na kungiyar ya shaida cewa jihohin 17 ne cikin 24 suka rattaba hannu akan takardar matakin da majalisar ta dauka, ya ce sun samu goyon baya da kaso mafi rinjaye inda na fiye da kaso biyu bisa uku na manbobin kungiyar inda a Arewa aka samu goyon baya 100 bisa 100 yayin da aka samu kaso 95 bisa 100 a jihohin Kudu maso Yamma, ya ce hasalima kungiyar bata aiki a jihar Edo inda korarran shugaban kungiyar ya fito biyo bayan almundahana da riginginmu da ya yi ta kulawa a yankin lamarin da yasanya gwamnatin jihar a wanccan lokacin ta dakatar da kungiyar a fadin jihar, ya ce Alhaji Musa Maitakobi zai ci gaba da rike matsayinsa na shugaban kungiyar a Legas da kuma shugabanin ruko na kungiyar a matakin kasa.

A ranar lahadin da ta gabata ne tsohon shugaban kungiyar Mista Osakpanwan Eriyo, ya bayyana rushe tsarin shugabancin kungiyar reshan jihar Legas inda ya ce, wa’adin su ya cika, kuma yana da ikon rushe su, lamarin da yaso ya kawo tashin-tashina ga kungiyar inda shugaban ta Legas Alhaji Musa Maitakobi da sauran mukarrabansa suka ce atafau basu rushe ba, domin wa’adinsu bai cika ba kamar yadda dokar kungiyar ya tanadar.

Mahukuntan jihar Legas sun yi zama da shugabannin kungiyar domin cimma daidaito da fatan ganin a magance barkewar rikici ko zubda jini.

Manbobin kungiyar a jihar Legas sun yi ta murna bayan hukuncin da majalisar zartarwar kungiyar ta yanke na bai wa Alhaji Musa Maitakobi jan ragamar kungiyar.