✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Maslaha ta karrama ‘ya’yanta

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Cigaban al’umma ta Masalaha da ke karamar Hukumar Birni a Jihar Kano ta karrama ‘ya’yanta inda ta…

A karshen makon da ya gabata ne kungiyar Cigaban al’umma ta Masalaha da ke karamar Hukumar Birni a Jihar Kano ta karrama ‘ya’yanta inda ta bayar da lamnbar yabo ga mutum 36.

Ita dai kungiyar Masalaha wacce ta kunshi Unguwanni 10 na cikin birni da suka hada da Marmaara da Alfinduki da Sheshe da kwalwa da Daneji da SabonSara da Sudawa da Kududdufawa da Akwa da jingau an kafa ta ne shekara 20 da suka gabata.

A Jawabinsa na maraba, Shugaban kungiyarKwamred Bashir Shu’aibu ya bayyana cewa kungiyar tana gudanar da wannan taro ne a duk shekara da nufin yaba wa ‘ya’yan kungiyar wadanda ke bayar da gudummuwa ga yankin ta fuskoki da dama.

Kwamare Bashir ya y i kira ga sauran ‘ya’yan kungiyar da su yi koyi da wadanan mutane da aka karrama wajen bayar da himma a bangaren da kowane mutum ya yi fice a ciki. “mun bayar da wannan lambar yabo ga wadannan mutane don yaba wa ayyuaknsu da hazakarsu, har ila yau kuma bayar da lambar zai zama wata dama ta karfafa gwiwar sauran al’ummar yankin ta yadda za su yi koyi da su wajen bayar da gududmmowarsu ga ci gaban yankin da kuma jama’armu gaba daya”

Da yake jawabi Shugaban Kwamitin Amintatau na kungiyar Group Captain Rufa’i D. Garba (mai ritaya) ya bayyana cewa tsawon lokacin da aka kafa wanann kungiya, mutane da dama sun amfana daga tallafin wanann kungiya ta banagarori daban-daban.

Rufa’i Garba ya bayyana damuwarsa game da yadda halin tabarbarewa da ilimi ya sami kansa a ciki, inda ya yi kira ga gwamnati da ta kai dauki ga lamarin ta hanyar ba wa ilimin firmare muhimmanci.  “kowa yana sane da halin ni-‘ya-su da ilimi yake ciki musamman ilimin firamare, wanda shi ne ginshiki. Za ka tarar malaman ba su da kwarewa, ba su da sha’awar aikin, kusan duk malamin da za ka gani a firamare to ya rasa aikin yi ne kawai. Ba kamar ada ba lokacin da malamanmu ke koyar da mu suna da sha’awar koyarwar. Don haka akwai bukatar gwamnati

ta tashi tsaye ta nema wa harkar mafita, matukar a na so a samar da al’umma ingantacciya, kasancewar abbu al’ummar da za ta ci gaba idan ba ta da ilimi” Daga cikin wadanda suka sami wannan lambar girmamawar sun hada da Kwamishinan Al’amuran Kudi na jihar Dokta Aminu Mukhtar  dan’amu da Mai rikon Mukamin Magatakardar Kwalejin Harkokin Shari’a ta Malam Aminu Kano da Dokta Mukhtar Musa Bako da Farfesa Mustapha I. Abdullahi da Dokta Auwalu Saminu da Alhaji Hamza Bala Baba da sauransu.