✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar manoman Najeriya za ta kafa bunkuna a shiyyoyin Arewa don tallafa wa manoma

Shugaban hadadiyar kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Malam Yakubu Ibrahim Iro ya ce kungiyarsu za ta kafa kananan bankuna masu sunan AFAN Micro Bank a shiyyoyin…

Shugaban hadadiyar kungiyar manoman Najeriya (AFAN) Malam Yakubu Ibrahim Iro ya ce kungiyarsu za ta kafa kananan bankuna masu sunan AFAN Micro Bank a shiyyoyin arewacin kasar nan don tallafa wa manoma. 

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da sababbin shugabannin riko na kungiyar na shiyyoyin arewa a garin Jos da ke Jihar Filato.
Ya ce “muna son mu kafa wadannan bankuna masu suna AFAN Micro Finance Bank a kowace shiyya ta arewacin Najeriya domin za su taimaka wa manoma wajen samar musu da rance don bunkasa aikin gona.”
Ya ce babban burinsu shi ne su taimakawa manoman Najeriya, domin yau a duniya babu abin da aka sanya a gaba kamar aikin gona.”
“Mun kaddamar da sababbin shugabannin na shiyyoyin arewa ne don ganin an sake farfado da ayyukan kungiyar a yankin arewa. Babu shakka wadannan sababbin shugabanni da muka kaddamar muna ganin mutane ne wadanda za su daukaka wannan kungiya a yankin arewa baki daya, don manoman yankin su sami damar cin gajiyar kungiyar.” Inji shi.
Ya nemi shugabannin su ya tsaya wajen ganin an gudanar da zaben shugabannin riko na jihohin shiyyarsu tare da tattara sunayen ‘yan kungiya a shiyyarsu. A kuma gudanar da zaben shugabannin wannan kungiya na riko a dukkan matakai kafin karshen wannan shekara.
A nasa jawabin a madadin shugabannin da aka rantsar, Alhaji Buhari Zakari ya mika godiyarsu ga kungiyar kan wannan damar da aka ba su.
Ya ce: “ Ina ba da tabbacin za mu sauke nauyin da aka dora mana kuma za smu yi iyakar kokarinmu wajen ganin mun daukaka wannan kungiya. Za mu shiga lungu da sako na arewacin Najeriya wajen ganin mun yada ayyukan wannan kungiya.”
Shugabannin da aka rantsar su ne Misis Christie Sunkur da Ahmed Bako Doma a matsayin shugaba da mataimaki a shiyyar Arewa ta Tsakiya. Alhaji Buhari Zakari da Alhaji Hayatu Liman a matsayin shugabannin kungiyar a shiyyar Arewa ta Yamma, Umar Abubakar da Rebaran Moses Gideon a matsayin shugabannin kungiyar a shiyyar Arewa ta Gabas.