’Yan kungiyar malaman makaranta ta Najeriya reshen Jihar Barno ta bukaci gwamnatin tarayya ta agaza musu sakamakon halin da suka tsinci kansu dalilin hare-haren ’yan Boko Haram a jihar.
Shugaban kungiyar Alhaji Bulama Abiso ne ya bukaci hakan a lokacin da ya tattauna da Wakilin Aminiya a Maiduguri a ranar Talata.
Ya ce: “Hare-haren da Boko Haram ke kai wa a Jihar Borno sun haifar da durkushewar ilimi, musamman ma a makarantun firamare da na karamar sakandare, inda maharan ke kai hari a wadannan makarantu suna kona azuzuwa, su kuma kashe malamai, inda alkaluman kididdiga ke nuna cewar maharan sun kashe malaman makaranta kimanin 250, tare da kona makarantu sama 100 a fadin jihar a cikin shekara 3. Don haka ina fata gwamnatin tarayya za ta taimaka mana don saukaka wa rayuwar ’yan kungiyarmu.”
Ya ce saboda rashin tabbas da kuma firgici da tsoro da malamai da dalibai suka samu kansu a ciki ne, ya sanya gwamnati ta rufe makarantu a jihar, inda duk da cewa a yanzu an bude, to ana bukatar agazawar gwamnati sosai.
“Babu shakka sha’anin ilimi a jihar nan ya samu koma baya sosai, inda sai an dauki dogon lokaci kafin ya dawo daidai, don haka muna bukatar gwamnatin tarayya ta shigo cikin shirin bunkasa ilimi a wannan jiha tamu ta Borno, domin gwamnatin Jihar Borno ba za ta iya wannan abu ita kadai ba. barnar da wadannan maharan suka yi mai yawa ce a cikin lokaci kadan, dole sai an dauki dogon lokaci kafin a gyara, misali sun kone mafi yawan makarantun firamaren da ke fadin jihar, a kuma kusan dukkan kananan hukumomin jihar 27, duk da cewar gwamnatin jiha na bakin kokarinta, to amma fa akwai kayayyakin aiki da wasu muhimman abubuwan da suka kamata a ce makarantu sun mallaka.
“Wadannan mahara sun kashe mana malaman makarantu akalla 250 a cikin shekara 3, wannan ya nuna muna bukatar wadanda za su maye gurbinsu, to kusan za a ce sun gurgunta harkar ilimi a jihar nan, inda tabbas ake bukatar tallafin gaggawa daga gwamnatoci da kuma masu kudi wajen ganin an mayar da ababen da aka rasa a wannan jiha tamu.” Inji shi.
Ya ce babban kalubalen da ake fuskanta a yanzu shi ne iyayen dalibai sun kasance cikin fargabar cewa za a iya kashe’ya’yansu idan suka tafi makaranta.
Ya ce kungiyarsu ta taimaka wa iyalan mambobinsu da aka kashe.
“Iyalan mamata 50 za su ci moriyar Naira 200,000 a cikin wata 3, inda muke kyautata zaton hakan zai agaza wa rayuwarsu. kungiyarmu da ke yankin Arewa maso Gabas za ta bada gudunmawar Naira 200,000 ga wasu iyalan mamatan 50 nan gaba, don a tabbatar da cewar ko wani iyalin mamaci ya amfana da wannan tsari namu.” Inji shi.
kungiyar malaman makaranta a Barno ta bukaci gwamnatin tarayya ta agaza musu
’Yan kungiyar malaman makaranta ta Najeriya reshen Jihar Barno ta bukaci gwamnatin tarayya ta agaza musu sakamakon halin da suka tsinci kansu dalilin hare-haren ’yan…