Mai karatu ina fata zuwa yau da ka ke karanta wannan makala, kungiyar Malaman jami`o`i ta kasa wato ASUU, ta janye yajin aikin da suke yi tun ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata kusan watanni biyar, yajin aikin da yake shi ne na biyu mafi tsawo a tarihin yajin aikin da `yan kungiyar suka saba yi, tun bayan na shekarar 1996, a lokacin da marigayi Dokta Mohammed Tahir Liman yana Ministan Ilmi a gwamnatin marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha, lokacin da `yan kungiyar ta ASUU, suka share watanni shidda cur suna yajin aiki.
karfin gwiwar da nake da shi na kungiyar ta ASUU, ta yi shelar janye yajin aikin na watanni biyar, bai rasa nasaba da irin taron da Kwamitin zartaswa na kasa baki daya da kungiyar ta yi a Kano a ranar Juma`ar da ta gabata, taron da kungiyar ta so yi tun a ranar 5 ga wannan watan, amma mutuwar tsohon shugabanta na kasa Farfesa Festus Iyayi na Jami`ar Benin a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da shi akan hanyar Lokoja zuwa Abuja a ranar 4 ga wannan watan akan hanyarsa zuwa Kano, don halartar taron Kwamitin zartaswar kungiyar a Kano tasa ce ta sa aka daga wancan taro zuwa mako uku. Taron da kungiyar taki ta ce da Manema labarai uffan, akan kudurorin da ta cimmawa bare ranar da za ta janye yajin aikin.
Makasudin yajin aikin wannan karon, shi ne kungiyar ta nemi lallai sai gwamnatin tarayya ta amince tare da fara aiki da yarjejeniyar da suka sa hannu da ita a shekarar 2009, bayan wani yajin aiki da suka yi a waccan shekarar. Wasu daga cikin bukatun da waccan jarjejeniya ta kunsa, akwai batun a shekarar 2012, gwamnatin taryya zata bayar da tsabar kudi har Naira biliyan 100, ga jami`o`in don su bunkasa ayyukan koyo da koyarwa, al’amuran da suka hada da gine-ginen dakunan daukar karatu da na kwanan dalibai, da na bincike da gwaje-gwje da makamantansu. Kuma tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, gwamnatin tarayyar za ta sake bayar da tsabar kudi Naira biliyan 400, ga jami`o`in don ci gaba da samar da irin wadancan bukatu da na ambata tun farko. Wasu batutuwa da ke kunshe a yarjeniyar su ne biyan alawus-alawus ga Malaman da sauran Ma`aikatan jami`o`in, biyan alawus-alawus din da zasu kunshi biyan bashin na baya.
A lokacin wannan yajin aiki duk wani wanda ya isa kama daga Sarakunan gargajiya da shugabannin addinai dana al`umma dasauran masu ruwa da tsaki akan harkokin ilmi da masu mulki, kai hatta shi kanshi shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ba wanda bai roki `yan kungiyar ta ASUU, da su wa Allah, suwa Annabinsa da su hakura su koma bakin aiki, musamman a lokacin da gwamnatin tarayya ta yi wa kungiyar ta ASUU tayin basu Naira biyan 100, don samar da ingantuwar koyo da koyarwa a jami`o`in da kuma Naira biliyan 30, don rage alawus-alawus din Malaman jami`o`in, amma dai suka tushe kunnuwansu, ta yadda kullum idan sun ji wadancan kiraye-kiraye, sukan nemi masu yinsu da su roki gwamnatin tarayya da ta biya masu bukatun da suka nema, musamman akan batun inganta harkokin koyo da koyarwa a jami`o`in kasar nan, lamarin da suka ce sun tabarbarewar da suke bukatar agajin gaggawa. Dadin dadawa kungiyar ta ASUU ta yi zargin cewakafin da bayan ta fara yajin aikin, ta rubutawa Mahukunta wasikun tuni har sau 351, da yin zama 150, da jami`an gwamnatin tarayya da aniyar kar ma su shiga yajin aiki, ko kuma yadda zasu kawo karshen yajin aikin bayan sun fara shi.
Duk da wancan hamzari da Malaman jami`o`in suki ta kafawa, har gobe akwai “yan kasa da suke zarginsu da cewa sun kafe akan yajin aikin ne, don kawai abinda zasu samu na bukatun kansu, wasu kuma suka rinka zargin `yan kungiyar ta ASUU da ita kanta gwamnatin tarayya da cewa sun yi biris akan wanna yajin aikin ne don kawai `ya`yansu basa karatu a jami`o`in kasar nan.
A yanzu maganar da ake ciki, ko ba kome, ta tabbata cewa Malaman jami`o`in sun yi nasarar samun amincewar gwamnatin tarayya na zata aiwatar da karin alawus-alawus dinsu, kamar yadda jarjejeniyar shekarar 2009, ta kunsa. Alal misali daga yanzu alawus din duk wani Malami da zai duba dalibai fiye da biyar a wurin da aka turasu don koyon aiki ko koyarwa kanta, ko kuma shi Malamin ne zai je wata Cibiya don karo ilmi, to, za a rika ba Farfesa ko mai neman zama Farfesa (Reader) N100,000. Babban Malami za a rika bashi N80,000, Malami da Mataimakin Malami za a rika ba su N60,000, dukkan wadannan alawus-alawus za a rika biyansu ne sau daya a shekara. Dadin dadawa kuma inda Malami zai gudanar da aikinsa ne a wajen garin da jami`arsa take, alawus dinsa zai kuma kunshi biyan kudin maleji da na kwanan daji da ake ba ma`aikacin gwamnati.
Wani alawus din da za a rinka biyan Malaman jami`o`in sun hada dana daukar wasu nauye-nauye da basa cikin ayyukansa nayau da kullum. Akan haka jarjejeniyar ta 2009, ta tanadi a rinka ba Mataimakin shugaban jami`a N750,000, ya yin da shugaban Tsangaya da Darakta za a rinka basu N500,000, mukaddashin shugaban jami`a da mataimakin tsangaya, za a rinka basu N350,000, mai biye da mataimakin tsangaya da shugaban sasheza a rinka biyansu N250,000. Mai karatu haka wannan alawus zai kasance har ya zuwa sauran jami`an jami`a da za a rinka ba su wadannan alawus-alawus duk shekara zuwa mafi karanci na N150,000, duk shekara.
Akwai ma alawus din aikin bayan lokaci da za a rinka biyan Malaman jami`ar akan karin kowace awa da suka yi. Mai karatu in takaice maka labara, na ji wani ma`aikacin jami`a yana cewa yajin aikin ya biyasu, don a fadarsa akwai wanda za a biyakudaden baya na wadannan alawus-alawus da sauran `yantsarabe-tsare da zai tashi da Naira miliyan goma. Tirkashin! Ka ji mai karatu. Amma lokacin da ake yajin aikin kungiyar ta ASUU, ta kafe akan cewa ba don kashin kanta take yajin aikin ba, to yanzu dai ta tabbata ga abinda zasu samu, duk da yake ta yi kokarin ganin janyo hankalin gwamnatin tarayyar na ta kara kudaden tafiyar da jami`o`in. Al`amarin da zamu zuba idanu mu ga ya ya zasu kasance. Fatan mu Iyaye dai ita ce kungiyar Malaman jami`o`in da gwamnati karsu fake da wannan yajin aiki su kara kudaden karatu, da ka iya sa dalibai su ma su shiga nasu yajin aikin. Allah Ka ba mu shugabanni da za su rinka tausaya mana, amin summa amin.
kungiyar Malaman Jami’o’i ta samu biyan bukata kenan?
Mai karatu ina fata zuwa yau da ka ke karanta wannan makala, kungiyar Malaman jami`o`i ta kasa wato ASUU, ta janye yajin aikin da suke…