Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) ta maka Ministar Al’adu da Kirkira, Hannatu Musa Musawa a kotu kan zargin rashin kammal yi wa kasa hidima (NYSC).
Sashen kare hakki na kungiyar (NBA-SPIDEL) ya garzaya kotu ne bavan ka-ce-na-ce da aka yi a 2023 cewa an nada Hannatu Musawa a mukamin minsta ne a yayin da take aikin yi wa kasa hidima.
Tun da farko dai Kungiyar Marubuta Kan Kare Hakkin Dan Adam (HURIWA) ta fara bayyana cewa bai halasta ga Hannatu Musawa ta zama minista ba, a alhali tana tsaka da aikin yi wa kasa hidima.
A cewar kungiyar, Hannatu Musawa ta jingine aikinta na yi wa kasa hidima a Jihar Ebonyi a shekarun baya, amma daga bisani ta dawo domin kammalawa a 2023, inda aka turo ta aiki a wani kamfanin aikin lauya.
Daraktan yada labaran hukumar NYSC, Eddy Megwa, dai ya ce aikin ministan da Hannatu Musawa take yi ya saba Dokar NYSC.
Megwa ya shaida wa wakilinmu cewa an nada ta minista ne alhali tana da ragowar wata hudu kafin kammala NYSC, kuma doka ta haramta wa masu yi wa kasa hidima karbaraikin gwamnati har sai sun kammala hidimar kasa ta shekara guda.
NBA-SPIDEL da ke karar Hannatu da Gwamnatin Tarayya, na neman Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayyana ko Hannatu Musawa na da hurumin zaba wa kanta lokacin yin NYSC.