kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta shirya taron tattaunawa da kungiyar ’yan jarida marubuta labaran cutar shan inna (Journalist Against Polio) domin kara musu karfin guiwa game da yadda za su ci gaba da wayar da kan jama’a don a kawo karshen yaki da cutar cikin gaggawa.
Taron, wanda ya gudana a Otel din Zaranda da ke Bauchi, ya gayyaci shugabannin kafafen watsa labarai da kungiyoyin ’yan jarida domin zaburar da su wajen ganin sun kara himma kan aikinsu na wayar da kan jama’a.
Cikin jawabinsa, mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Alhaji Sagir Aminu Saleh ya yaba game da irin gudummowar da kafafen watsa labarai ke bayarwa ta hanyar wayar da kan jama’a game da fitowa don karbar allurar rigakafin cutuka masu nakasa yara. Ya ce gwamnatinsu na kashe makudan kudi wajen yaki da cutar shan inna.
Dokta Adamu Ningi, wakilin kungiyar lafiya ta duniya, cikin jawabinsa ya bayyana cewa ana sa ran kammala yaki da cutar shan inna zuwa cikin shekara mai zuwa, daga nan kuma za a dauki yaki da wasu cututtuka irin na bakon dauro da makamantansu. Ya bukaci iyaye su rika fitowa da yaransu domin amsar allurar rigakafin da ake yi saboda a dakushe tasirin bazuwar cututtuka. Ya bukaci ’yan jarida su kara himma kan aikinsu na wayar da kai game da yadda mutane za su gamsu da ayyukan hukumar lafiya ta duniya da gwamnatoci saboda a samu nasarar inganta lafiyar jama’a.
Jami’ar hulda da ’yan jaridu a kungiyar ta WHO, Madam Moji Afolabi, ta bayyana cewa an samu nasara a kan aikin wayar da kan jama’a game da amincewa da allurar rigakafi, don haka yanzu ba a samun tirjiya kamar yadda ake samu a baya, kuma hakan na faruwa ne game da gudummowar da kafafen watsa labarai da jama’a ke bayarwa kan aikin.
Shugaban kungiyar ’yan jarida ta jiha, Malam dahiru Garba ya yaba wa kungiyar lafiyar wajen taimaka wa kafafen watsa labarai game da yadda suke gudanar da aikinsu na wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya. Ya ce kungiyar a shirye take wajen kara wa ’ya’yanta karfin guiwa da ilmantarwa game da yadda za su inganta ayyukansu.
Ita ma shugabar kungiyar marubuta labarin cutar shan inna, Madam Elizabeth Carr, ta yaba da gudummowar da ’yan jaridun ke bayarwa na shiga lunguna domin shirya tarukan ilmantar da mazauna karkara al’amuran da suka danganci kiwon lafiya a jihar ta Bauchi.
kungiyar lafiya ta yi taro da kungiyar ’yan jarida kan foliyo
kungiyar lafiya ta duniya (WHO) ta shirya taron tattaunawa da kungiyar ’yan jarida marubuta labaran cutar shan inna (Journalist Against Polio) domin kara musu karfin…