Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta dakatar da yajin aikinta domin ci gaba da tattauna da gwamnati kan batun mafi karancin albashi.
Shugaban Kungiyar TUC, Festus Osifo, ne ya sanar da hakan bayan taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka gudanar a Abuja.
“Taron hadin gwiwa na majalisar zartarwar TUC da NLC ya amince a dakatar da yajin aikin nan take na tsawon mako guda,” in ji shi a wurin taron.
Nan gaba ake sa ran kungiyar za ta fitar da sanarwa a hukumance kan dakatar da yakin aikin na tsawon mako guda.
Bangarorin kungiyar kwadago karkashin jagorancin NLC sun yi zaman ne a Abuaj ranar Talata bayan gaza cimma matsaya da bangaren gwamnati kan batun mafi karancin albashi.
’Yan kwadago sun dakatar da yajin aikin ne domin ba sa damar tattaunawa na tsawon mako guda kamar yadda suka yi alkawari a tattaunawarsu da bangaren gwamnati a ranar Litinin.
Kungiyar ta shuga yajin aiki ne domin neman karin mafi karancin albashi sakamakon janye tallafi da ninka kudin wutar lantarki, tashin dala da faduwar darajar Naira hadi da ninkuwar farashin kaya a sanadiyar janye tallafin mai da gwamnatin kasar ta yi.
Yajin aikin dai ya tsayar da harkoki a asibitoci da makarantu da bankuna da kasuwanni da bangaren sufuri da makamashi sauransu a fadin Najeriya.
Daukacin kasar ya kasance a cikin duhu na sama da awa 36 tun vayab da yajin aikin ya yi sanadiyar katse babban layin wutar lantarkin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa a wata tattaunawar sirri da kungiyar ta yi da bangaren gwamnati a daren Litinin a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, sun cimma yarjejeniya cewa gwamnati za ta kara mafi karancin albashi daga Naura 60,000 da ta gabatar a zaman.
Bangarorin za su ci gaba da tattaunawa a kullum na tsawon mako guda domin cimma matsaya guda.
Ita kuma kungiyar za isar da sakon ga sauran kungiyoyin da ke karkashin inuwarta domin su dauki matsaya.
Hakazalika ba za a cutar da ma’aikatan da suka shiga yajin aikin ba.
Bayan nan ne kungiyar ta ce za ta sanar da matsayarta kan makomar yajin aikin idan ta kammala taron hadin gwiwa da sauran bangarorin da ke karkashin inuwarta.