✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar kwadago ta ja kunnen ’yan kasuwa

Shugaban kungiyar kwadago Jihar Gombe Kwamared Haruna Kamara ya ja kunnen ’yan kasuwar jihar masu hana shigo da Doya da sauran kayan Marmari saboda neman…

Shugaban kungiyar kwadago Jihar Gombe Kwamared Haruna Kamara ya ja kunnen ’yan kasuwar jihar masu hana shigo da Doya da sauran kayan Marmari saboda neman karawa kayan kudi.
Shugaban ya yi wannan jan hankalin ne a lokacin da ya jagoranci tawagar kungiyar kwadagon da sauran kungiyoyi a lokacin da suke zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin kudin wutar lantarki da kamfanonin samar da wutar lantarki suka yi.
Ya ce ’yan kasuwar Gombe suna hana masu Doya da suke kawowa daga jihohin Adamawa da Taraba da sauran jihohi har sai sun sayar da na su, inda ya ce hakan ba daidai ba ne ya ce hakan ke sa abinci ya yi tsada.
Hakazalika, masu kayan gwari irinsu Lemo da sauran nau’in kayan marmari suma ba sa bari a shigo da su har sai wanda yake kasa a kasuwar ya kare, inda ya ce hakan shi ke sa komai ya yi tsada.
Ya ce wadannan baki da suke shigo da Doya da sauran kayan abinci suna tsayawa ne a bayan gari suna shigowa su nemi sojoji su yi musu rakiya sannan su iya shigo wa Gombe su sayar da kayansu.
Ya ce: “Idan ’yan kasuwar nan ba su dai na ba, zan jagoranci tawagar kungiyar ’yan kwadago suje su kwashe kayan su rabarwa mutane kyauta kamar yadda suka yi a lokacin da masu gidajen mai suka boye mai. Wanda hakan ya sa aka bude gidajen mai din aka bai wa masu ababen hawa kyauta.”
Daga nan sai ya ce ya ba su mako guda su gyara, sannan ya ce nan gaba kadan zai yi zama da shugabanin ‘yan kasuwar don daidaita rashin jituwar da ke tsakaninsu.