Kungiyar kwadogo ta Najeriya NLC ta ce, a yau Talata ta fara wata gagarumar zanga-zangar gama gari don matsa lamba ga gwamnatocin Najeriya su amince da karin albashi mafi karanci na Naira dubu talatin.
Sakatare Janar na Kungiyar NLC Dakta Peter Ozo-Eson ya ce, shirin wannan zanga-zangar nada alaka jinkirin da aka samu wajen mikawa majalisar dokoki kudirin amincewa da biyan albashin Naira dubu 30.