✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar kishin APC ta shirya kwallon sada zumunci tsakanin Kwankwasiyya da Malam-madori SP Academy

A makon da ya wuce ne, kungiyar ’yan kishin Jam’iyyar APC a yankin Arewa maso  Yamma, ta shirya wasan kwallon kafa, tsakanin Kwankwasiyya da Malam…

A makon da ya wuce ne, kungiyar ’yan kishin Jam’iyyar APC a yankin Arewa maso  Yamma, ta shirya wasan kwallon kafa, tsakanin Kwankwasiyya da Malam Madori SP Academy, inda aka tashi kunnen doki.
Shugaban kungiyar na yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Umar dan Hadeja, ya bayyana wa Aminiya cewa, wannan wasa na sada zumunci ne tsakanin matasan jihoihin yankin, tare da yada manufofin fitar da Najeriya daga kangin da take fama da su a a halin yanzu. Don haka ya bukaci hatta su ’yan PDP su yi wa kansu kiyamul laili su shiga wannan tafiya don kyautata rayuwar daukacin al’ummar Najeriya.
“Mu adawarmu ba ta siyasa ba  ce, illa dai manufa ce tagari, wadda ke kokarin tafiya da kowa , ta yadda za a kare muradun daukacin al’ummar Najeriya. A kyautata wa talaka ya san gwamnati na yi da shi. Don haka nake kira ga ‘ya’yan jam’iya mai mulkida ke da kyakkyawar manufa su shigo wannan tafiya, ta yadda jam’iyyar APC za ta samu mulki a kowane mataki” inji shi.
Wannan wasa dai ya kayatar, inda matasa daga Jihar Kano suka hadu da takwarorinsu na Jigawa suka fafata.
Babban Sakataren kungiyar Kishin Jam’iyyar APC na kasa, Malam Musa Wakaso, ya yaba wa kungiyarsa, kan kwallon sada zumunci da ta shirya, tare da nuna goyon bayansa ga shugabancin Alahji Abubakar Lawal baure, wanda shi ne shugaba na kasa.
dan Hadeja, ya ce za a ci gaba da shirya irin wannan wasa, don jawo matasa, su shiga tafiyar kawo sauyi da kyautata rayuwar al’ummar kasa. Sannan ya yi fatan alheri ga daukacin iyayen Jam’iyyar APC, musamman Janar Muhammadu Buhari da Ahmad Bola Tinubu da sauran shugabanni.