✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Kiristoci ta yi tir da batun ba matasan Biniwai makamai

kungiyar matasan Kiristoci ta CYCP, wacce ke bin kadi da jaddada zaman lafiya a cikin al’umma ta yi Allah-wadai da kiraye-kirayen da wasu suke yi,…

kungiyar matasan Kiristoci ta CYCP, wacce ke bin kadi da jaddada zaman lafiya a cikin al’umma ta yi Allah-wadai da kiraye-kirayen da wasu suke yi, na cewa ya kamata a samar wa matasan Jihar Biniwai makamai domin su kare jihar.

Shugaban kungiyar, Rabaran Johnson Audu ne ya yi wannan bayani a yayin da yake ganawa da ’yan jarida a Abuja, a ranar Talata da ta gabata. Ya bayyana cewa irin wannan kira da wasu manyan kasa ke yi, musamman Shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Chif Paul Unongo, wanda ya ce al’ummar Biniwai za su hada kungiyar matasa, su ba su makamai domin kare jihar, bai dace ba, domin wannan barazana ce ga zaman lafiyar al’ummar kasa gaba daya.

Ya ce irin wadannan kiraye-kiraye za su iya dawo da hannun agogo baya, sannan su dakile kokarin da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki ke yi wajen samar da zaman lafiya a kasa.

“daukar matakin ramuwa cikin sauri da nufin magance tarzoma ko fitina ba hanyar Allah ba ce kuma hanya ce da ke haddasa koma-baya, wacce ba za ta haifar da da mai ido ba. Babu abin da irin wannan mataki ke nunawa sai bakaken halayenmu da rashin hakuri,” inji shi.