Shugaban kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Kebbi, Dokta Bashir Mohammed Gaci, ya bukaci hadin kai daga dukkan Katsinawa da Daurawa a jihar, domin kara dawo da martabar kungiyar kamar yadda take tun kafa ta shekaru ashirin da suka gabata.
Shugaban ya yi wannan kiran ne lokacin da yake jawabi a wani taron tattaunawa da aka yi a dakin taro na makarantar kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya ta Waziri Umaru da ke birnin Kebbi.
Dokta Bashir ya ce kiran irin wannan taro yana da amfani domin zai kara sa fahimtar juna da kuma karo dankon zumunci tsakanin ’yan kungiyar kuma shugabanninta da mambobinta kowa akwai gudummuwar da zai bayar domin cigabanta.
Ya kuma jawo hankalin ’yan kungiyar wajen ba shi hadin kai da goyon baya don ya sauke nauyin da suka dora masa cikin nasara.
A karshe ya yi kiran su kasance suna zuwa wurin taro a duk lokacin da aka kira taron, kuma ya bukaci wadanda ba su yi rijista da kunguyar ba su tabbatar da sun sami sakatare domin ya yi musu rijista kafin taro na gaba.
kungiyar Katsinawa da Daurawa a Jihar Kebbi ta nemi hadin kan ’ya’yanta
Shugaban kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Jihar Kebbi, Dokta Bashir Mohammed Gaci, ya bukaci hadin kai daga dukkan Katsinawa da Daurawa a jihar, domin kara…