kungiyar Kare Hakkin Yara kanana (Child Protection Network) a Jihar Gombe, za ta hada kai da malaman addini wajen ganin ta kare hakkin yara sannan kuma da yakar masu yi wa yaran fyade.
Shugabar kungiyar, reshen Jihar Gombe, Misis Grace Samuel ce ta bayyana haka ga wakilinmu, sannan ta yi nuni kan irin kalubalen da kungiyar ke fuskanta, wajen kokarinta na yakar dabi’ar yi wa kananan yara fyade.
Ta kuma ce wata matsalar har ila yau ita ce mafi yawan iyayen yaran ba sa daukar matsalar fyade a matsayin babbar matsala wacce take jefa ’ya’yan nasu cikin wani hali balle ma su yi tunanin zuwa kotu don kwato wa ’ya’yan nasu ’yancinsu.
Misis Grace, ta ce za su shigar da shugabannin addinai cikin harkokinsu saboda su dinga magana a kan wannan matsala, “Saboda a gaskiya babbar matsala ce wacce ta zama ruwan dare a wannan lokaci da muke ciki”. Inji ta.
A cewarta, sau da yawa akan samu matsalar yi wa yara masu karancin shekaru da ba su wuce uku zuwa bakwai ba fyade, amma iyaye na tsoron fitowa su fadi saboda suna gudun kada jama’a su san halin da ’yarsu ta shiga balle ma a yi tunanin hukunta masu yi din.
“Ba za mu bari irin haka ta ci gaba da faruwa a tsakanin al’umma ana kallo ba, dole mu tashi tsaye mu dauki matakin kare ’yancin ’ya’yanmu”, inji ta, cikin fushi da kaushin murya.
Misis Grace ta jaddada dalilin kafa kungiyar, wanda ya jibanci kare ’yancin yara kanana, sannan a ba su dukkan kulawar da ta dace a rayuwa. Sannan ta tabbatar wa iyayen yaran cewa matsala irin ta fyade za a dinga daukar mataki a kai na kai wanda ya aikata laifin gaban kotu ba tare da wanda aka yi wa din sun bayyana a gaban kotun ba.
Saboda haka ta roki iyayen yara su bar komai a hannunsu don ganin an hukunta duk wani mai yi wa yara fyade don hakan ya zama darasi ga sauran masu nufin yin irin wannan hali.
A karshe Misis Grace ta ce nan gaba kadan kungiyar za ta yi zama da duk masu ruwa da tsaki da malaman addinai da masu sarautar gargajiya don neman mafita.
kungiyar Kare Hakkin Yara ta yi damarar yaki da masu fyade
kungiyar Kare Hakkin Yara kanana (Child Protection Network) a Jihar Gombe, za ta hada kai da malaman addini wajen ganin ta kare hakkin yara sannan…