kungiyar kanikawa ta Jihar Katsina (NATA) ta bukaci mambobinta su tsare gaskiya dangane gyarar abin hawa da jama’a suke kawo musu, sannan kungiyar ta sha alwashin ci gaba da koya wa matasa sana’o’in hannu.
Sabon shugaban kungiyar Alhaji Sani Dogo ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa mambobin kungiyar jawabi a makon jiya bayan sun zabe shi shugabancinta.
Ya ce koyar da sana’o’in za su taimaka wajen kawar da zaman kashe wando da shaye-shaye, inda a karshe ke jefa rayuwar matsasa a cikin hadarin da ke kai su ga aiwatar da ayyukan ta’addaci.
Shugaban kungiyar ya tabbatar wa mambobin kungiyar cewa, ba zai yi kasa a gwiwa wajen ganin cewa sun amfana da abubuwa da dama da kungiyar za ta yi ba.
Ya ja hankalin ’yan kungiyar su ci gaba da rike amanar dukiyoyin jama’a da aka mika musu ta hanyar gyara.
Ya ce “kungiyarmu tana sane da irin bata-garin da ake samu a ko’ina ba wai a wajenmu ba kadai, kuma muna sa ido har sai mun kai ga kakkabe su.”
Ya bukaci gwamnatin Jihar Katsina ta yi musu rijiyar burtsatse biyu a filinsu wanda tuni har sun fara gina ofishin gudanarwar kungiyar.
A karshe ya mika godiyarsa ga gwamnatin Jihar Katsina bisa jagorancin gwamna Shema a kan dukkan gudunmuwar da ta ba kungiyarsu.