✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Jarumai da Gora ta Hayin Banki za ta koma aiki

A gobe ne kungiyar Jarumai da Gora, wadda ke da alhakin samar da zaman lafiya a Unguwar Hayin Banki da kewaye da ke Kaduna za…

A gobe ne kungiyar Jarumai da Gora, wadda ke da alhakin samar da zaman lafiya a Unguwar Hayin Banki da kewaye da ke Kaduna za ta koma bakin aiki bayan dogon hutu.

Kwamandan kungiyar, Auwal Aliyu wanda aka fi sani da GOC ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya, inda ya ce za su koma aiki ne bayan sun gabatar da wasu gyare-gyare da za su canja yanayin da ake gudanar da kungiyar, sannan kuma bisa yadda suke samun koke-koken mutane da suke bukatar su koma aiki.

“Mun yanke shawarar dawowa ne saboda mutanen gari suna bukatar dawowarmu. Mutane da yawa suna ta kira suna tambaya a kan cewa wai ya ake ciki ne. Kuma kasancewar aiki ne na mutane, duk lokacin da mutanen da kake yin aikin dominsu suka ce ka taimaka musu, dole ka ci gaba da musu aiki koda kuwa ba ka so.”

Ya kara da cewa za su fara ne da zagaye na musamman, inda za su zagaya tare da sojoji da ‘yan sanda domin su sanar da mutane cewa sun dawo bakin aiki, kuma za su ci gaba ne daga inda suka tsaya. 

Daga karshe sai ya yi kira ga mutanen Hayin Banki da su ba su hadin kai domin ci gaba da samar da zaman lafiya da mutunta juna.