kungiyar zaman lafiya ta Jamnati Fulbe ta kasa ta yi babban taro a garin Eggua, yankin da yake fama da rikicin makiyaya da manoma a Jihar Ogun, inda sarakunan Fulani da jama’arsu daga jihohi 6 na Kudu maso Yamma suka halarta tare da wakilan hukuma da jami’an tsaro, don samar da maganin sabanin makiyaya da manoma.
A jawabinsa na maraba, Sarkin Eggua, Oba Michael Adeleye Dosunmu ya bayyana murnarsa da taron, wanda ya hada manoma da makiyaya, “Wadanda su ne a kan gaba wajen samar da abinci. Saboda haka ya zama wajibi ku yi maganin sabanin da ke tsakaninku domin amfanin kanku da kasa baki daya”. Inji shi.
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan kammala taron, shugaban kungiyar, Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu Kadiri ya ce kungiyar tana karkashin kungiyar Miyetti Allah ne, ba kamar yadda wasu ke hange ba. “Babbar manufar kungiyar Jamnati Fulbe ita ce samar da zaman lafiya tsakanin mutanenmu makiyaya da jama’a, musamman manoma. bullar kungiyarmu sauki ne ga kungiyar Miyetti Allah ta fannoni daban-daban, musamman idan mun dauki matakan da suka dace, sannan mu sanar da shugabannin Miyetti Allah da suke kusa da mu.” Inji shi.
A jawabin sakamakon bayan taro, shugaban reshen kungiyar na Jihar Ogun, Alhaji Abubakar Ibrahim Dende ya ce cikin abubuwan da aka tattauna akwai batun samar da katin shaida ga ’ya’yan kungiya don tantance su daga bakin haure; da yin godiya ga gwamnatin jihar kan aikin samar da burtaloli ga makiyaya, kodayake akwai wasu sauran bukatu da za a mika a rubuce. Sannan da amincewar halartar babban taron da za a yi a ranar 27 ga watan gobe a fadar Uban kungiya na kasa, mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Sulu Gambari. “Haka nan, mun dauki matakan gyara kura-kuran bangaren mu makiyaya, a cikin gida, kafin a kai ga na manoma.” Inji shi.
Tun farko, mai masaukin baki, Sarkin Fulanin Eggua, Alhaji Adamu Ibrahim Oloru, wanda ya shugabanci taron, ya tunatar da muhimmancin cudanya da juna, wanda ke kulla zumunci a tsakanin al’umma. Ya bukaci makiyaya su girmama dokokin kasa da kyautata zamantakewa da jama’a, lamarin da zai taimaka wa martabar Fulani. “Ina roko ga ’yan kalilan cikinmu da suka samu ilmin zamani su dage, tsakani da Allah, su bullo mana da sababbin dabarun koyar da ’ya’ya da jikokinmu, domin an bar mu a baya. Rashin wadatar ilmin addini da na zamani matsala ce a tsakaninmu da jama’a. Ina rokon hukuma ta taimaka mana ta wannan fanni domin mu sami habakar kiwon dabbobinmu, wanda zai taimaka wa bunkasar tattalin arzikin kasa,” inji shi.
kungiyar Jamnati Fulbe ta yi taron magance sabanin makiyaya da manoma
kungiyar zaman lafiya ta Jamnati Fulbe ta kasa ta yi babban taro a garin Eggua, yankin da yake fama da rikicin makiyaya da manoma a…