✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Izala za ta hada kai da gidauniyar Zakka a Gombe

Lamido, ya yi alkawarin bai wa kungiyar gurbin samun horo a gidauniyar ta zaka da wakafi da take gudanarwa.

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis sunnah (JIBWIS) reshen Jihar Gombe karkashin shugabancin Injiniya Salisu Muhammad Gombe da shugaban Majalisar Malamai Sheik Abubakar Lamido Abubakar, ta yi alkawarin hada kai da Gidauniyar Zakkah da Wakafi dan gudanar da aikace-aikacen tare.

Shugaban kungiyar Izala, Injiniya Salisu Muhammad Gombe, ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar da suka kai ofishin gidauniyar da ke harabar tsohon Masallacin Modibbo Bubayero da ke fadar jihar.

Ya ce makasudin ziyarar tasu shi ne bayyana kansu ga shugabannin gidauniyar su kuma sanin manufofi da aikace-aikacenta don ganin ta inda kungiyar za ta shigo domin yin hadin guiwa.

Ya kara jinjina wa gidauniyar bisa ga irin ayyukan madalla da ta yi wajen bada tallafi ga marasa galihu da kuma yadda take raba zakah a jihar.

A nasa jawabi tun farko, shugaban gidauniyar, Ustaz Abdullahi Abubakar Lamido, ya jinjina wa kungiyar ta Izala sannan ya ce za su ci gaba da yin ayyuka tare da ita da sauran kungiyoyi.

Lamido, ya yi alkawarin bai wa kungiyar gurbin samun horo a gidauniyar ta zaka da eakafi da take gudanarwa.

%d bloggers like this: