Shugaban Gudanarwa na kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Abdul-Nasir Abdul-Muhyi, ya bayyana cewa a cikin shekaru 38 da kungiyar ta yi da kafuwa.
Ya ce ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa
harkokin ilimi a kasar nan da kasashen ketare. Sheikh Abdul-Nasir Abdul-Muhyi ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe gasar karatun Al-kur’ani mai girma karo na 19 da reshen kungiyar na karamar hukumar Jos ta Arewa ya shirya.
Ya ce daga lokacin da aka kafa wannan kungiya zuwa yanzu shekaru 38 da suka gabata, kungiyar ta yaye mahaddata karatun Al-kur’ani dubbai da malaman addinin Musulunci da malaman fikihun Musulunci da kuma wadanda suka yi karatu a fannoni daban-daban, a makarantun kungiyar.
Ya ce a makarantar School for Higher Islamic Studies da ke garin Jos kadai akwai dubban mata wadanda suke garin da suka samu damar yin karatu.
“Akwai wata mata daya daga cikin daliban wannan makaranta yanzu haka malamar jami’a ce a Jami’ar Jos. Akwai doktoci da suka yi karatu a wannan makaranta da dama a wurare daban-daban a nan Najeriya da kasashen waje. Wannan ya nuna gagarumar gudunmawar da wannan kungiyar Izala take bayar kan harkokin ilimi,” inji shi.
Daga nan, ya yi addu’ar fatan alheri ga wadanda suka shirya wannan gasar karatun da kuma wadanda suka shiga gasar.
A nasa jawabin Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar reshen Jihar Filato Dokta Hassan Abubakar Dikko, kira ya yi ga masu hali kan su rika taimaka wa malaman addini kan halin kuncin rayuwar da suke ciki.
Ya ce “bai kamata a ce Allah Ya wadata ku ba, amma limamanku da malamankun masu yi maku wa’azi suna cikin halin wahala ba.”
Tun da farko, a jawabin Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar reshen karamar Hukumar Jos ta Arewa, Ustaz Muhammad Haris Shehu, ya bayyana cewa wannan gasar karatun da suka yi mako guda suna gabatarwa, ‘yan takara maza da mata guda 131 ne suka fafata.
Ya ce wadanda suka zamo zakara a kowanne mataki, a cikin matakai bakwai su ne zasu wakilci karamar hukumar a gasar karatun Alkur’ani ta jiha da za a gudanar nan ba da dadewa ba.
Salim dalhatu ne ya lashe gwarzon shekara. Har ila yau, an
raba kyaututtukan akwatinan talabijin da rediyoyi da atamfofi da shaddoji da sauran kyaututtuka ga wadanda suka zamo zakaru a gasar.
kungiyar Izala tana ba da gudunmawa don bunkasa ilimi – Sheikh Abdul-Nasir
Shugaban Gudanarwa na kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Abdul-Nasir Abdul-Muhyi, ya bayyana cewa a cikin shekaru 38 da kungiyar ta yi…