kungiyar Izala, reshen Jihar Legas ta tara fiye da Naira miliyan uku don daukar dawainiyar tafsirin da malami za su gabatar a fadin jihar a cikin watan azumi.
An gudanar da taron neman tallafin kudin ne a masallacin Bakon Nana da ke Agege, a karshen makon da ya gabata, inda attajirai da (sauran) ’yan kasuwa suka ba da gudunmawa daban-daban.
Da yake jawabi jim kadan kafin a kaddamar da gidauniyar, shugaban majalisar malamai na kungiyar, Malam dalhatu Abubakar Abdullahi ya ce, kungiyar na neman tallafin fiye da Naira miliyan 10 don daukar nauyin malami da za su gabatar da tafsiri a lunguna da sako-sako na jihar.
Malam dalhatu Abubakar, wanda ya ja hankalin masu kudi kan yawaita alheri a watan azumi, ya nemi jama’a su ba da tallafi mai tsoka domin daukaka addinin Allah.
Shi ma shugaban kungiyar na Jihar Legas, Alhaji Abubakar Gambo ya yi godiya ga Allah da kuma jama’ar da suka amsa gayyatar kungiyar.
Ya ce, “Babu shakka ka gayyaci jama’a kuma su amsa gayyatar taka wani abu ne. Saboda haka ina mai nuna farin cikina dangane da yadda na ga jama’a sun taru a wannan wuri don taimaka wa addinin Allah”.
Ya yi fatan Allah Ya karbi gudunmawar da aka bayar, Ya sanya albarka ga duk wanda ya bayar da dukiyarsa da ma wanda bai bayar ba.
Shi ma mataimakin shugaban majalisar malamai na jihar, Malam Buhari Yakub ya yi kira ga masu hannu da shuni su yaki shaidan domin ba ya son su aikata alheri.
“Yanzu a nan shaidan ya turo kungiyarsa domin su hana jama’a alheri. Saboda haka sai mun yake shi in dai muna so mu yi alheri sosai”. Inji shi.
Rassan kungiyar da ke kananan hukumomi da daidaikun masu kudi da ’yan kasuwa sun ba da gudummawa mai yawa inda reshen Agege na kungiyar ya ba gudumawa mafi tsoka ta fiye da Naira dubu dari biyar.
… Ta reshen Jihar Gombe ta kaddamar da gidauniya
Rabilu Abubakar, Gombe
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Jama’átu Izalatil Bid’á Wa Ikamatis Sunnah, reshen Jihar Gombe, Sheik Hamza Adamu Abdulhamid, ya ce hadewar kungiyar waje daya ya kawo wa musulmi ci gaba a kasar nan.
Shiek Hamza ya bayyana hakan ne a lokacin da kungiyar ta kaddamar da gidauniyar Naira miliyan sittin da biyar don ciyar da ilimi gaba da sayen motoci da sauran kayayyakin aiki na sakatariyar reshen.
Ya ce duk bayan mako bibbiyu, a matakin kanananhukumomi kungiyar tana taron tattauna yadda za cigaba. “Yanzu haka muna da makarantar renon yara da ta firamare da
sakandare, wadda ita ce kan gaba wajen samun sakamakon jarrabawa a Jihar Gombe. Sannan muna da makarantar da ke bayar da takardar shaidar difloma da NCE, wadanda dukansu sai da kudi za a ciyar da su gaba”. Inji shi.
Babban mai kaddamarwa, Alhaji Abdulkadir Hamma Saleh, kafin ya bayar da gudumawarsa, ya yaba wa jagororin kungiyar kan dunkulewarsu. Ya yi alkawarin ci gaba da bai wa addinin
Allah gudumawa a ko da yaushe, ba sai a irin wannan lokaci na gidauniya ba. Sannan ya yi kira ga musulmi su hada kai wajen cigaba da tallafa wa addinin Musulunci. Ya ba da gudumawar Naira miliyan goma tare da wasu Naira miliyan daya da dubu dari shida da hamsin da ya karbo daga wajen abokan sa.
Uwargidan tsohon gwamnan jihar, Hajiya Yelwa Goje, ta aiko da kyautar
Alkur’ánai 200 da sallaya 40 da kuma carbi 300; Sanata danjuma Goje ya bayar da Maira miliyan uku; Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tarayya Usman Bayero Nafada shi ma ya bayar da Naira miliyan uku.
Fiye da Naira miliyan talatin da hudu ne aka tara, amma kudi a hannu Naira miliyan shida ne da dubu dari takwas da goma, inda aka samu cakin Naira miliyan goma, sai masu alkawari na Naira miliyan goma sha bakwai.
Taron, wanda shi ne irinsa na farko da kungiyar ta shirya tun dunkulewarta, ya samu halartar manyan malamai na kungiyar na kasa.
Kwamitin Da’awa na masallacin Badar ya yi taron wa’azi
Adamu Umar, a Kubwa, Abuja
Kwamitin Da’awa na Masallacin Badar da ke Kubwa, Abuja ya shirya wani taron wa’azi, wanda aka yi wa taken “taimakon addinin Musulunci, hakkin kowane Musulmi ne”, don karsasa al’umma dangane da muhimmancin bayar da taimako wajen daukaka matsayin addinin da kuma kyautata zamantakewa a tsakani.
Taron, wanda ya sami halartar al’ummar musulmi da dama, ciki har da shugaban kungiyar Izalatul bid’a wa ikamatus sunna na kasa, Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya gudana ne a ranar Lahadin da ta gabata.
Babban sakataren kasa na kungiyar ta Izala, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, shi ne wanda ya gabatar da wa’azin, inda ya bayyana cewa al’ummar yankin Kudu maso Kudu, wato Neja-Dalta, su ne al’umma mafiya sauki wajen karbar Musulunci a kan sauran yankunan Najeriya.
Malamin ya ce a zagaye da yake yi na aikin da’awa a duk mako, wanda bai gaza na tafiyar kilomita dubu biyu zuwa yankuna daban-daban na kasar nan, ya fahimci cewa, “yankin (Neja-Dalta) na gaba wajen samun nasararar masu rungumar addinin Musulunci, sai dai inda matsalar take bayan sun musulunta, a mafi yawan lokuta, sai a samu wasu daga cikinsu sun koma dabi’unsu da suka baro bayan musuluntar, wasu kuma su bar ma addinin dungurugum”. Inji shi.
Ya danganta aukuwar lamarin da rashin daukar nauyin malamai da za su ci gaba da koyar da sabbin musuluntar yadda za su gudanar da bautarsu. Da wannan misalin ne ya yi nunin akwai bukatar a tashi tsayen wajen bayar da tallafin kudi da kayan aiki don daukan nauyin masu karantarwar da kuma gudanar da sauran hidindimu, don samun yadda za su tabbata a cikin addinin.
Irin wannan taron wa’azi, kwamitin da’awar kan shirya shi a duk wata uku, kamar yadda sakataren kwamitin, Malam Usman Ali Sani ya shaida wa mahalarta. Haka nan yana daga cikin ayyukan da ya tsara yi daga farkon shekarar nan zuwa karewarta, kai ziyarar gidajen kurkukun Kuje, da na Suleja. Sai kuma ziyarar wasu kauyukan Abuja da kewaye, inda ya gina masallatai da kuma makarantun Islamiyya don karantar da jama’ar yankunan.
A jawabinsa, Shugaban kwamitin, Alhaji Nuhu Bukar ya ce ayyukan da suke yi a gidajen kurkukun sun hada da jawo hankalin masu laifi da su rungumi rayuwa tagari bayan kammala wa’adinsu; da kuma yin belin wadanda aka tsare na tsawon lokaci ba tare da an yanke musu hukunci ba, kuma ba su da wanda zai yi belinsu.
Haka nan ya ce suna kai ziyara asibitoci don taimaka wa mabukata.
Shi kuwa shugaban kungiyar Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau kira ya yi ga kowane musulmi da ya kasance jakadan Musulunci nagari a duk inda ya samu kanshi. Haka nan ya ce akwai bukatar kowane masallaci da ya kafa gidauniya ta musamman don kulawa da marayu da sauran mabukata.
A jawabinsa na godiya, limamin Masallacin Badar, Imam Abdulmumini A. Khalid ya bayyana jin dadinsa da halartar malamin da ya gabatar da wa’azin, wanda ya ce a kullum cikin gayyata yake na tarurrukan wa’azi.
Fityanul Islam ta bukaci malamai su guji la’ántar juna
Rabilu Abubakar Gombe
kungiyar Fityanul Islam ta kasa, reshen Jihar Gombe ta yi kira ga malaman addini na dukkan bangarorin nan su guje wa kalaman batanci da zai haifar da rashin zaman lafiya ko rudani a lokacin tafsirin watan azumi.
Mataimakin Sakataren yada labaran kungiyar na kasa, wanda kuma yake sakataren yada labarai na Jihar Gombe, Alhaji Babawuro danmusa Abubakar, shi ya bayyana hakan a wata takarda da ya aike wa manema labarai a Gombe.
kungiyar ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su ninka kokarinsu wajen daukar nauyi ana sanya tafsiran da malamai suka gabatar a kafafen yada labarai na rediyo da talabijin na jiha da na kasa baki daya.
Sannan kungiyar ta yaba wa gwamnan jihar, Alhaji Muhammad Ibrahim Hassan dankwambo, bisa kulawar da yake bai wa kungiyoyin addinai a jihar ba tare da nuna bambanci ko bangaranci ba.
Kamar yadda kungiyar ta fadakar tun farko, ta bukaci malamai masu wa’ázi su yi shi kamar yadda Alkurá’ni da hadisan Manzon Allah SAW suka koyar don neman dorewar zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.
Har ila yau kungiyar ta yaba wa gwamnan na yadda ya nada wakilan hukumar jin dadin Alhazai na jihar wadanda suke da kwarewar da ta dace.
Sakataren yada labaran ya ce yana da kyau gwamnatin tarayya ta rage kudin zuwa aikin hajji saboda masu karamin karfi su sami dama su sauke farali.
Haka nan kungiyar ta gode wa ’ýan majalisar dokoki na jihar bisa yadda suka nuna damuwarsu dangane da matsalar da ma’áikata suke fuskanta na cunkoso da daukar tsawon lokaci ba tare da sun sami albashinsu a bankuna idan aka yi albashi.