kungiyar Izala reshen Jihar Bauchi ta kai ziyara ga Sarkin Bauchi Alhaji Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a fadarsa da ke Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake zantawa da manema labarai , Sheikh Nasir Abdulmuhiyi ya bayyana cewa shugaban majalisar malamai na kasa Sheikh Sani Yahaya jingir ne ya ba da umarni da a ziyarci sarkin a fadarsa domin sanar masa cewa a bana ma kungiyar ta sake turo Sheikh Nasir domin ya gudanar da tafsiri a babbar masallacin juma’a na Bakin Kura da ke Bauchi.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya nuna godiyarsa bisa yadda ake gudanar da tafsirin bana “lami lafiya ba tare da wata matsala ba.” Sarkin ya kara da cewa muna fatan a badi za a sake aiko sheikh Nasir domin ya gudanar da tafsiri a masallacin.
Har ila yau, Malamin ya bukaci sarkin da ya yi kira da babbar murya ga sabon Gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar da ya “rika biyan ma’aikata albashinsu domin kowa ya san cewa jihar Bauchi an dogara da albashi ne,” inji shi.
Daga karshe kungiyar ta nuna goyon bayanta bisa matakin da gwamnatin tarayya ta fara dauka a kan ’yan kungiyar Boko Haram da ke tada kayar baya a yankin Arewa-maso-Gabas.