Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta bude sabuwar sakatariyar da ta gina a garin Jos babban birnin Jihar Filato, a karshen makon jiya.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar Malamai ta kasa ta kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce kungiyar ta gina sabuwar sakatariya ce saboda yadda ayyukan kungiyar na yada addinin Musulunci ya kankama a Najeriya da kasashen waje.
Ya ce don haka kungiyar ta gina sabuwar sakatariyar da ta kunshi ofisoshi daban-daban da za a rika amfani da su, wajen gudanar da ayyukan kungiyar.
Ya mika godiyarsa ga dukan wadanda suka ba da gudunmawa wajen gina wannan sabuwar sakatariya. Sannan ya yi kira ga dukan rassan kungiyar su yi koyi da uwar kungiyar wajen gudanar da irin wannan aiki.
A jawabin, Gwamnan Jihar Bauchi Barista M. A. Abubakar ya taya Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir murna kan gina sabuwar sakatariya da kungiyar ta yi.
Gwamnan wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Addinin Musulunci ta Jihar Ustaz Muhammad Auwal Ibrahim ya wakilta ya yi fata Sheikh Sani Yahya Jingir zai kara zage damtse kan abubuwan da yake yi, na taimaka wa wannan kasa wajen tsayar da matasa kan hanya.
Taron ya samu halartar manyan sarakuna da ’yan siyasa da shugabannin kungiyar daga kowane bangare na kasar nan.