✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Ittihadu ta bude dukkan makarantunta

Shugaban kungiyar Makarantun Islamiyya ta Jihar Filato [Ittihadu Anwaril Hidayat], Alhaji Yusuf Yahaya ya bayyana cewa ya zuwa yanzu kungiyar ta sake bude dukkan makarantunta…

Shugaban kungiyar Makarantun Islamiyya ta Jihar Filato [Ittihadu Anwaril Hidayat], Alhaji Yusuf Yahaya ya bayyana cewa ya zuwa yanzu kungiyar ta sake bude dukkan makarantunta da ke garin Jos da kewaye, a sakamakon zaman lafiyar da aka samu.
Ya bayyana haka ne kuwa a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, sannan ya kara da cewa, “A lokacin da aka sami rikice-rikice a garin na Jos, akwai unguwanni da dama da muka rufe makarantunmu, saboda wasu an kona su, wasu an lalata su, wasu kuma mutanen da ke wajen sun tashi. Amma a yanzu mun  gyara wadannan makarantu mun sake bude su, sakamakon zaman lafiyar da aka samu. Mun yi amfani da kudaden gudunmawar da muka samu bara, a wajen kaddamar da neman gudunmawar da muka yi,  mun gyara makarantunmu guda 31”.
Ya ce sun sami nasarar  sake bude wasu sababbin makarantun a garin na Jos da kewaye da garin Bokkos da marabar Abuja, kuma a shekarar da ta gabata kungiyar ta sami gayyata zuwa wajen wani taron zaman lafiya na duniya da aka gudanar a kasar Ghana.
Alhaji Yusuf ya bayyana a bana ma  sun shirya gasar haddar karatun hadisan Manzon Allah [SAW] kamar yadda suka saba a kowace shekara, a inda suka sami gagarumar nasara. “Babban burinmu shi ne mu kafa babbar sakatariyar wannan kungiya a garin Jos”. Inji shi.
Sai dai ya koka kan yadda gwamnatin Filato ba ta taimaka wa kungiyar tasu, duk da daruruwan makarantun da suke da su da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ilmintar da matasa. Don haka ya yi kira ga gwamnatin ta Filato ta taimaka wa kungiyar a fannonin da suka kamata.
A karshe ya yi kira ga iyayen yaran da suke makarantun kungiyar su kara kaimi wajen taimaka wa makarantun.