kungiyar Injiniyoyi ta kasa ta bayyana kudurinta na bude rassanta a dukkanin kananan Hukumomi 775 da ake da su a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar ta kasa, Mista Otis Oliber Anyaeji ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da reshen kungiyar ta karamar hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna.
Bukin kaddamarwar, wanda aka gudanar da shi a Otel din Wonderland da ke Kafanchan, ya samu halartar shugaban kungiyar ta Jihar Kaduna Mista Abdurrasheed Babalola.
A cikin jawabin shugaban na kasa, Anyaeji ya bukaci sababbin shugabannin da su rungumu dukkanin membobin kungiyar wajen ganin ayyukansu na tafiya daidai kamar yadda ya kamata.
A jawabinsa, Abdurrasheed Babalola, ya bayyana cewa Allah Ya albarkaci garin Kafanchan da injiniyoyi wadanda suke matukar kokari wajen ganin ci-gaban al’umma.
“ina mai shawartar dukkanin injiniyoyin da ke wannan yankin da ku hada kawukanku waje daya wajen bayar da gudummawa don ci gaban kasa. Babu wata kasa a duniya wacce ta sazmu ci gaba ba tare da injiniyoyi ba.” In ji shi.
Shi ma sabon shugaban kungiyar na karamar hukumar Jama’a, Injiniya Musa Tete yayi alkawarin yin aiki tukuru tare da bin ingantattun tsare-tsare da za su cicciba kungiyar zuwa matsayin da ya dace cikin kankanin lokaci.
Musa Tete, ya yabawa shugaban kungiyar ta kasa da ya samu halartar wannan kaddamarwa da kan sa inda kuma ya bayyana masa cewa a shirye su ke su sadaukar da lokacinsu wajen tabbatar da kyawawan mafarke-mafarken da ya ke yi wajen bayar da kyakkyawan shugabanci abin koyi.
A karshe, babban bako na musamman a wajen taron, Mista Duchi Ganji, ya bayyana cewa kungiyar injiniyoyi ta kasa ita ce lemar da ta tattaro dukkanin injiniyoyin da ke fadin tarayyar Najeriya baki daya, waje guda.