✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar direbobin tifa ta Jihar Gombe ta zabi sababbin shugabanni

kungiyar  Direbobin Tifa ta Jihar Gombe ta gudanar da zaben sababbin shugabanninta, inda Alhaji Saleh Mabel ya sake zama shugabanta, ba tare da hamayya ba.A…

kungiyar  Direbobin Tifa ta Jihar Gombe ta gudanar da zaben sababbin shugabanninta, inda Alhaji Saleh Mabel ya sake zama shugabanta, ba tare da hamayya ba.
A lokacin da yake zantawa da Aminiya, Alhaji Saleh Mabel ya ce yana ganin kyakkyawan shugabancin da ya gudanar a karon baya, ya sa ya sake lashe zaben, wanda zai shugabanci kungiyar na wasu shekaru hudu a karo na biyu.
A cewarsa, lokacin da yake shugabantar kungiyar karo na farko, ya kawo wa kungiyar ci gaba masu yawa, wadanda tunda kungiyar ta kafu, fiye da shekaru goma sha biyu, ba ta samu irinsa ba. “Gamsuwa da kyawun shugabanci da kuma adalcin da aka nuna a tsakanin mambobin kungiyarmu, ya sa sauran abokan takara da ni suka janye min. Sun nuna ba za su yi takara da ni ba, saboda sun san zan kara kawo wa kungiyar ci gaba mai yawa,” inji shi.
Alhaji Saleh, ya kara da cewa kafin ya zama shugaban kungiyar, wasu sun zama, amma sai dai ba su yi abin da ya yi a shekara hudun farkon nan ba, lamarin da ya sa ’ya’yan kungiyar suka ji dadi suka sake zabar sa don ya ci gaba.
Ya nuna godiyarsa ga mambobin kungiyar kan yadda suka nuna masa kauna da karamci kuma suka sake ba shi dama don ya shugabance su. “Ba na shugabanci da karfi ko yadda na ga dama. Ina aiki ne da la’akari da abin da mambobinmu suke so, musamman dayake ina shugabantar kungiyar jama’a ne,” inji shi.
Alhaji Saleh ya yi alwashin zai kara kawo ci gaba mai ma’ana ta fuskar bayyana matsayin kungiyar da kuma ’ya’yanta.
Yayin da yake zayyana wasu daga cikin nasarorin da ya samu a lokacin shugabancin nasa, Alhaji Saleh ya ce, “Mun yi wa kungiyar rijista da gwamnatin jiha, lamarin da ya sa duk abin da gwamnatin Jihar Gombe za ta yi da kungiyoyi, tana yi da mu, kuma takan ba mu duk taimakon da ya kamata.
“A baya kungiyar ba ta taba mallakar mota ba, amma a karkashin shugabancina ta samu mota, wacce da ita ake zuwa taron wata-wata da akan yi a Abuja, kuma da ita ake gudanar da aikace-aikacen kungiyar a duk lokacin da bukatar haka ta taso”. Inji shi.
A karshe ya nemi gwamnati ta sama musu ofis mallakarsu na dindindin, domin a halin yanzu wanda suke ciki, an ba su aro ne.
Sauran masu rike da mukamai da za su rufa masa baya sun hada da: Iliyasu Muhammad, mataimakin shugaba; sai Abdulkadir Aliyu, Ma’aji;  sai Hamza Abubakar, Sakataren mulki da Muhammad Dauda Gambo, mataimakinsa; sai Yaya Muhammad, mai bincike na 1 da Abdullahi Waja, mai bincike na 2.
Sauran sun hada da Kabiru Isah da Hassan Abdullahi da Ahmed Kumo, a matsayin Trusty na 1 da na 2 da na 3 (wato kwamitin dattawa); sai Umar Babayo, Jami’in kula da jin dadi; sai Dauda Malami, Jami’in hulda da jama’a (P.R.O. 1) da Dala Kaltungo P.R.O. 2; sai Salihi Garba, Jami’in kula da abin hawa (b.I.O. 1) da Isma’ila B. Waja Billiri, b.I.O. 2; da kuma Abdullahi Inusa, wanda ya zama Sakataren Kudi.