kungiyar Deborah Foundation ta raba zannuwa da yadudduka da sabulai ga marasa galihu da ke zaune a gundumomi 34 na karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna.
kungiyar ta kaddamar da shirin raba wa marasa galihu wadannan kayayyakin ne a ranar Asabar da ta gabata a garin Saminaka.
Da take jawabi a wajen raba kayayyakin, Shugabar kungiyar Deborah Foundation Misis Deborah Musa Kane ta ce, sun raba kayayyakin ne sakamakon halin da marasa galihu suke ciki.
Ta ce a shirinsu na farko sun tallafa wa daliban makarantun firamare 1020, inda suka raba musu kayayyakin karatu da rubutu da unifom a wannan karamar hukuma.
Ta ce baya ga shirin tallafa wa marasa galihu suna da shirin tallafa wa al’umma don su dogara da kansu ta hanyar koya musu sana’o’i.
Ta ce “A shirinmu na tallafa wa al’umma don su dogara da kansu, tuni mun ba mata rancen kudi a matsayin jari, wanda ya kama daga Naira dubu 5 zuwa Naira dubu 50 don su kama sana’o’i. Mun ba mata sama da 200 rance, sannan mun ba matasa 25 rancen Babura duk a karamar Hukumar Lere.”
Misis Deborah ta ce babban burinsu shi ne su tallafa wa gajiyayyu da marayu, su kuma tallafa wa al’umma don su dogara da kansu, inda dalilin hakan ne ya sa suka kafa kungiyarsu a shekara ta 2009.
Ta bukaci masu hannu da shuni su rika tallafa wa gajiyayyu da marayu don a samu ingantacciyar al’umma.