Kungiyar Ci Gaban Yankin Funtuwa da ke Jihar Katsina ta koka kan matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da shi a yankin. Shugaban Kungiyar, kuma Limamin Masallacin Gidajen ’Yan Majalisar Dokoki ta Kasa da ke Zone B, Apo, Babban Birnin Tarayya Abuja, Imam Ibrahim Awwal [Usama] ne ya bayyana kukan kungiyar, lokacin da yake zantawa da jaridar Aminiya.
Ya ce a halin da ake ciki al’ummar yankin sun shiga cikin mawuyacin hali, sakamakon rashin wutar lantarki da ake fuskanta a yankin.
Ya ce al’ummar yankin sun dogara da wutar lantarki ce wajen gudanar da sana’o’in walda da nika da sauran sana’o’i daban-daban, amma saboda rashin wutar; yanzu sun zama ba su samun damar gudanar da wadannan sana’o’i.
Imam Usma ya ce akwai lokacin da masu nikan inji suka yi yajin aiki a yankin, saboda matsalar rashin wutar lantarki.
“Kamfanonin da suke rarraba wutar lantarki, babu abin da suka sani, sai dai su karbi kudin wuta daga jama’a; alhalin ba sa bayar da wutar. Ya kamata kamfanonin da aka bai wa dillacin sayar da wutar lantarki a Najeriya su san mutuncin jama’a,” inji shi.
Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta karbe bayar da wutar lantarki daga kamfanoni masu zaman kansu. Kuma ta tsaya wajen ganin ta samar da tsayayyiyar wutar lantarki a Najeriya wadda al’ummar Najeriya za su yi amfani da ita, don samun abin da za su dogara da kansu.
Ya yi kira ga kantomomin yankin Funtuwa da Sanatan yankin da ’yan Majalisar Tarayya da suka fito daga yankin Funtuwa su taimaka, su dauki matakan da suka wajaba don ganin an warware wannan matsala ta rashin wutar lantarki a yankin.