✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar CAbE ta yi wa ’yan jarida bitar tasirin fina-finan fadakarwarta

Dokta Abiodun Adeniyi, daya daga cikin jiga-jigan fafutikar kawar da tashe-tashen hankula a kasar nan, ya gabatar da jawabi kan ayyukan kungiyar CAbE da ke…

Dokta Abiodun Adeniyi, daya daga cikin jiga-jigan fafutikar kawar da tashe-tashen hankula a kasar nan, ya gabatar da jawabi kan ayyukan kungiyar CAbE da ke kokarin kawar da tsattsaurar manufar tayar da hankalin al’umma da fadace-fadace a ganawarsa da ma’aikatan kafafen yada labarai.

A wajen taron wanda aka gudanar a Otal din Hawthorn da ke Garki Abuja, Jami’in gudanarwar kungiyar ta CAbE, tare da Dokta abiodun Adeniyi sun amsa tambayoyi daga ’yan jarida, sannan an nuna fina-finan da kungiyar ke amfani da su wajen fadakarwar kan matsanancin tashin hankali da fadace-fadace da ake fama da su a kasar nan. Fina-finan dai sun nuna wa al’umma illar da ke tattare da fadan kabilanci da na addini, sannan suka bai wa al’ummar da suka gayyato don kallon fina-finan suka yi sharhi.

“Wannan kungiya ta CAbE bat a gwamnati ba ce, sannan ta fara gudanar da ayyukanta a Janairun 2017, inda take ta kokarin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan, t ahanyar kawar da matsanancin tashin hankali da ke haifar da salwantar rayuka da dukiya,” inji shi.

Mafi yawan masu sharhi kan fina-finan sun danganta fadace-fadacen kabilanci da na addini da ke faruwa a kasar kan yadda aka kyale matasa babu aikin yi, wasu ma ba su samu damar yin karatun zamani da zai ba su damar dogaro da kai ko samun ayyuka a hukumance, ballantana a kamfanoni masu zaman kansu.

Fina-finban da aka fi amfani das u wajen fadakarwar sun hada na Turancin Ingilishi da aka yi kan mummunar illar da rikicin Boko Haram ya yi wa al’umma a yankin Arewa maso gabas, sai kuma wani kan gadon gabar iyaye da kakanni da aka yi cikin harshen Hausa, mai taken “GABA Tushen Ta’asa.”

A cewar Dokta Abiodun, kungiyarsa na amfani da sabon salon fadakarwa a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta na intanet, wadanda suka hada da facebook da twitter da whatsapp.

Dokta Abiodun ya amsa tambayoyi biyu daga wakiliyar kafar sadarwa ta Premiumtimes da wakilin jaridar Dailytrust. Fatima Bashir ta yi tambaya kan yadda za a tantance irin tasirin da wayar da kai da fadarwar kungiyar CAbE ta yi wajen shawo kan tashe-tashen hankula a kasar nan. “Ko za a iya tabbatar mana da irin tasirin da fadakarwar CAbE ta yi wajen sanya jama’a su yi aiki a aikace don shawo kan fadace-fadace da tashe-tashen hankula a kasar nan?”

Shi kuwa Mista Onamisi Alao na jaridar Dailytrust cewa ya yi, “bayan wannan ganawa da aka yi da ’yan jarida, inda aka tattauna kan ayyukan kungiyar CAbE, shin za a ci gaba ko an kammala ken an?

Game da amsoshin tambayoyin da aka bijiro da su Dokta Abiodun ya ce: “Za a iya gnin tasirin ayyukanmu na fadarwa a hankali, a hankali. Domin ba rana guda ake iya kaiwa ga nasara ba, amma barna ana iya yenta ta yi mummunan tasiri lokaci guda.”

Tambaya ta biyu kuwa sai  cewa ya yi, “aikin fadakarwa yanzu aka fara har sai an kai matsayin tantance nasara, ta yadda mutane za su fahimci illar da tashe-tashen hankula ke yi wa rayuka da dukiya.

A karshen wannan taro, Dokta abiodun da Mista Tunde Ashawolu sun jagoranci mahalarta taron wajen kaddamar da rigar kungiyar CAbE mai daude da sakon tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, ta hanyar kudurin kokarin kawar da m atsanancin tashin hankali da kabilanci da bambance-bambance marasa tushe da suka damfaru a zukatan al’umma. Sakon da ke jikin rigar a harshen Ingilishi ma’anarsa: kokarin shawo kan matsanacin tashin hankali ya faro daga garemu.”

An dai raba wa mahalarta taron wadannan riguna da faya-fayan fina-finan fadakarwa kan illolin da ke tattare da tashe-tashen hankula a kasar nan.