✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar banga ba kishiyar jami’an tsaro ba ce- Ali Sakkwato

kungiyar ’yan Banga ta Najeriya mai suna bigilant Group of Nigeria (bGN) ta gudanar da wani babban taro na kasa a hedikwatar kungiyar da ke…

kungiyar ’yan Banga ta Najeriya mai suna bigilant Group of Nigeria (bGN) ta gudanar da wani babban taro na kasa a hedikwatar kungiyar da ke Kaduna a makon jiya. Aminiya ta tattauna da Kwamanda-Janar din kungiyar Alhaji Ali Sakkwato, inda ya bayyana cewa yadda suka kafa kungiyarsu da kuma matsalolin da suke fuskanta . Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya:  Ga shi yau kun yi wani babban taro na kasa, ko za ka gutsura mana tarihin kafa wannan kungiya ta bGN?
Ali Sakkwato:  Babu shakka kwamandojin kungiyar ’yan Banga ta kasa sun yin taro na musamman, inda muka tattauna wasu muhimman batutuwa na kara bunkasa ta da samar da yanayi mai gamsarwa wajen tafiyar da ita. Na ji dadin ganin yadda wakilai daga dukkan jihohin kasar nan suka halarci wannan zama bisa sa kai da kishin ci gaban ita kanta kungiyar da inganta tsaro a kowane sako na kasar nan, musamman ganin cewa duk jihar da ka je za ka ga ’yan kungiyarmu suna taimaka wa hukumomin tsaro a wurare daban-daban.
Kafa kungiyar mu ya samo asali ne a wani zamani can baya, inda a yankinmu na Tudun Wada a Kaduna aka rika aikata ayyukan barna, kuma kowa ya shiga damuwa bisa wannan al’amari, wanda nan take kwamishinan ’yan sandan Jihar Kaduna na wancan zamani ya umarci kowane DPO da ke yankin Gidan Gayu da Hakimin Tudun Wada marigayi dan Lawan don su dauki matakin gaggawa wajen kawar da duk wani abu na laifi a wannan yanki.
Wannan ta sanya muka fara gudanar da taro domin bullo da hanyoyin magance wadannan abubuwa da suke damun mu, inda muka hadu da su Alhaji  Ahmadu Chanchangi da sauran manyan yankin, hakan ne ya jawo kafa kungiyarmu, wadda yanzu ake ganin ta a ko’ina a kasar nan tana aikin tabbatar da tsaro.
Aminiya:  A wancan zamani ta yaya kuka fara gudanar da aiki?
Ali Sakkwato: Babu shakka mun sha fama kafin mu samu daidaituwar al’amuran wannan kungiya, domin aiki ne na sa kai ba wani abu ake samu ba illa taimakon kai da kai. Don haka duk wadanda kake gani suna aikin banga to suna yi ne domin taimaka wa al’umma ba biyan su ake yi ba, duk da cewa yanzu  wasu gwamnatoci suna tallafa wa ’yan kungiyar a yankunansu da alawus da kuma kayan aiki kamar tocila da batura, amma har yanzu muna bukatar taimako daga gwamnatin tarayya da na jihohi.
Aminiya:  Kasancewar ka daya daga cikin mutanen da suka kafa kungiyar banga, wace gudummawa ka bayar wajen ci gabanta ke nan?
Ali Sakkwato:  Ina so ka sani cewa na kashe duk kudina domin ganin kungiyarmu ta kafu, kuma ta dore, tun daga wancan zamani har zuwa yau din nan.  A da ina da tankunan daukar mai har guda 35 amma duk sun kare  kan aikin kungiya. Ba zan iya kiyasta kudin da na kashe a kan kungiyarmu ba. Alhamdulillah,  ga shi ta zamo abar misali wajen tabbatar da tsaro a kasar nan, wannan yana yi mini dadi kwarai.
Aminiya: Ina batun yi wa kungiya rijista?
Ali Sakkwato: Gaskiya mun dade kwarai muna ta fafutukar yin rijista, amma ba mu samu yi ba, sai a zuwan tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo a shekara ta 1999. Kuma daga wannan lokaci ne muka samu amincewar gwamnatin tarayya, kuma muke aiki a kowane sako na kasar nan.
Yanzu al’umma ta yi yawa, kuma hukumomin  tsaro suna  bakin kokarinsu wajen kare lafiya da dukiyoyin  jama’a, amma  yana da kyau mu ci gaba da tallafa masu wajen ganin an hada hannu domin kara inganta tsaro da tabbatar da bin doka a kasa musamman Najeriya.
Aminiya: Ko kana samun wani taimako daga gwamnatoci  tun da na ga ayyukan naku suna da amfani ga al’umma?
Ali  Sakkwato: Gaskiya ba ma samun taimako  daga gwamnati a matsayin tallafi ga kungiyar bigilant, sai dai kamar yadda na fada maka a baya, ana dan taimaka wa ’ya’yan kungiyar da alawus a wasu jihohin da kananan hukumomin, amma gundarin taimako ga uwar kungiya ba mu taba samu ba, kuma muna da bukata kwarai.
Aminiya: A wannan taro na ga wakilai daga jihohin Kudu da Yamma da kuma Gabas, ta yaya kuka kawo su?
Ali Sakkwato: Duk wanda ka gani a wannan wuri shi ne ya kawo kansa domin kishin kungiyar. Babu wanda muka bai wa kwabo domin ya zo taro, ga shi kuma ka ga an yi cikar kwari, kuma mun tattauna muhimman abubuwa na inganta tsaro a kasa baki daya. Kuma ina so jami’an tsaro su sani cewa muna aiki ne kawai domin mu taimaka kan harkar tsaro a unguwanni da sauran wurare ba kishiyoyinsu ba ne.
Aminiya: Mene ne matsalolin da suke damun ku ke nan?
Ali Sakkwato: Abubuwan da suke damun kungiyar bigilant suna da yawa, kuma an ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, amma muna da bukatar motocin sintiri da sauran kayan aiki kamar na sadarwa da na’urorin tattara bayanai da sauransu. Sannan muna kira ga masu hali da su fara taimaka wa kungiyarmu, domin tana da matukar muhimmanci  gare mu baki daya. Haka kuma ina kara karfafa wa matasanmu gwiwa da su kara jajircewa wajen yin aikin kungiyar bigilant, domin aiki ne na lada.
Aminiya: Ko kana da wani sako ga al’umma da kuma gwamnatoci?
Ali sakkwato: Sakona dai shi ne, a kara hada hannu wajen  gudanar da aiki saboda kishin kasa da kuma inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan, kowa ya sani cewa sai da zaman lafiya ne ake cimma nasara, don haka ina jinjina wa daukacin ’yan kungiyarmu da hukumomin tsaro da gwamnatocin da ke taimaka wa ’yan kungiya  tare da yin kira da a kara taimaka wa kungiyar bigilant Group a duk inda take.