Cibiyar Bunkasa Ilmi da Wayar da Kan Jama’a (AWEDI) da ke Jos, babban birnin Jihar Filato, ta raba wa marayu 95 na Jos da kewaye da Tilden Fulani a karamar Hukumar Toro ta Jihar Bauchi shinfaka da turamen atamfa da shaddoji suka gudanar da bukukuwan sallah.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala raba tallafin, daraktan cibiyar, Sheikh Muhammad Sulaiman ya bayyana cewa an ba kowane yaro tufafin sallah da kuma shinkafa.
Ya ce, “Kamar yadda ka sani, mun sanya mayarun a makarantun a inda wasu masu hali suke taimakawa wajen biyan kudaden makarantun, musamman Alhaji Aliko dangoto, wanda ya dauki nauyin biya wa 55 daga cikinsu kudaden makaranta. Sannan a kodayaushe muna bin yaran muna karfafa masu gwiwa a kan muhimmancin karatun da suke yi a makarantun. Kuma mun zadi wasu daga cikinsu muna koya masu sana’o’in hannu”.
Dangane da matan da mazajensu suka mutu kuwa, daraktan ya ce suna tallafa musu da abubuwan rage radadin rayuwa. “Aikin tallafa wa marayu da irin wadannan mata, ba aiki ne na mutum daya ba, aiki ne na al’umma gabaki daya, don haka muna kiran masu arziki da kungiyoyi su zo a tallafa. Akalla a rubuce muna da marayu sama da 3,000”.
kungiyar AWEDI ta raba wa marayu 95 tallafi
Cibiyar Bunkasa Ilmi da Wayar da Kan Jama’a (AWEDI) da ke Jos, babban birnin Jihar Filato, ta raba wa marayu 95 na Jos da kewaye…