Wata sabuwar kungiya mai suna ‘Arewa Initiatibe for balue Adbancement and Adbocacy (AIbADAC)’, ta gudanar da taron bita don fadakar da jama’a kan illar shaye-shayen kayan maye.
Da yake jawabi jim kadan da kammala taron, wanda aka gudanar a filin wasa na harabar barikin sojojin ruwa da ke Apapa a Jihar Legas, shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Aliyu Ibrahim ya ce taron ya zama dole saboda la’akari da halin da matasa suka shiga sakamakon shaye-shaye.
Ya ce, “Idan ka duba za ka ga harkar shaye-shaye ta zama ruwan dare gama duniya. Matasa sun tsunduma a ciki gadan-gadan, saboda haka sai muka yi tunanin wace hanya za mu bi domin fadakar da jama’a illar wannan lamari. Saboda haka muka yanke shawarar kiran taron bita na kwanaki biyu don mu wayar da kan matasa kan illar shaye-shaye. Muna so duniya ta san cewa illar shaye-shaye ta yi kamari a tsakanin matasa, shi ya sa birinmu shi ne mu ga cewa mutane sun daina wannan mummunar dabi’a, musamman matasan”.
Ya ci gaba da cewa, za su zagaya domin fadakar da jama’a. Za mu fara tun daga wurin taron har zuwa kan mahadar Bega-suya. Kuma za mu ci gaba da yin tattaki muna shiga lungu-lungu har tsawon kwanakin uku don fadakar da jama’a illar shaye-shaye kuma ba za mu daina fadakar da jama’a ba, har sai mun cimma burinmu na ganin mutane sun daina shaye-shayen kayan maye da shan muggan kwayoyi”.
Shi ma mai magana da yawun kungiyar na kasa, Alhaji Sagiru Ibrahim Bichi ya bayyana cewa muhimman abubuwan da kungiyar ta sanya a gaba su ne wayar da kan jama’a kan matsalar shaye-shaye da ciwon fuka da ciwon kanjamau da sauran cututtuka.
Ya bayyana cewa babban kalubalen da ke gaban kungiyar shi ne yadda za ta sami goyon baya da isassun kudin da za ta rika gudanar da ayyukanta.
Wani matashi wanda yake shaye-shaye mai suna Sallau ya bayyana farin cikinsa dangane da bitar da kungiyar ta shirya.
Ya ce, “Babu shakka ina shan tabar wiwi, amma zuwana wannan taro na karu da abubuwa da yawa kuma daga yau ba zan kara shan tabar wiwi ba domin na fahimci cewa cutar kaina nake yi’.
Jami’i na hukumar NDLEA, Mista Akpan D. Akpabio ya ilimantar da mutane ire-iren kayan maye da suke da illar ga lafiyar dan Adam.
Sarakuna daban-daban sun yi jawabi a wurin taron bitar sannan mutane da dama sun yi tamabayoyi ga jami’in hukumar NDLEA kan muggan kwayoyi.
kungiyar ‘Arewa Initiatibe’ ta yi taron bita kan illar shaye-shaye
Wata sabuwar kungiya mai suna ‘Arewa Initiatibe for balue Adbancement and Adbocacy (AIbADAC)’, ta gudanar da taron bita don fadakar da jama’a kan illar shaye-shayen…