✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiyar Annahada na ba da agajin farko a dukkan duniya – Kwamanda Sani Musa

Aminiya: Gabatar mana da kanka? Da farko sai ka yi mana bayani game da wannan kungiya taku ta Annahada, shin mene ma’anar sunanta? A takaice…

Aminiya: Gabatar mana da kanka?

Da farko sai ka yi mana bayani game da wannan kungiya taku ta Annahada, shin mene ma’anar sunanta?

A takaice dai kungiyar nan an kafa ta tun 1953. Maulanmu Sheik Sharif Ibrahim Saleh ne ya kafa ta. Bayan ya kafa ta, sannan ya nemi izini wurin Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyas da ya kafa ta a nan Najeriya. Aka yi masa izini kuma tun daga nan ne shi kuma Sheikh Sharif Saleh ya kafa ta a nan Najeriya. Kafin a kafa ta a nan ma sai da aka fara kafa ta a kasashen Larabawa kamar Syria da Masar da kuma Sudan da Libya. Annahada kungiya ce da take yada manufofin addinin Musulunci da kuma aikin agaji da kuma da’awah da kuma sauran ayyuka na addinin Musulunci.

Ko yaushe ne ta shigo nan Najeriya?

Ba zan iya mantawa ba, a shekara ta 2003 Maulanmu Sheik Sharif Ibrahim Saleh ya kirawo ’yan Najeriya zuwa Maiduguri, cikin watan Maulidi, a wani gagarumin taro da aka hada na kafa Annahada. Ke nan wanda Alhamdulillahi, ni ina daya daga cikin mutanen da suka je wannan taro. Tun daga wannan lokaci maulanmu ya umarci ’yan Najeriya da su zo a je a yada kungiyar da kuma manufofinta.

Akwai kungiyoyin addinin Musulunci daban-daban da ake da su a Najeriya, me ya bambanta Annahada da sauran kungiyoyin da ake da su?

Akwai bambanci tsakanin kungiyar Annahada da sauran kungiyoyin addinai. Dalili kuwa shi ne, ita Annahada kungiya ce ta duniya, kungiya ce wadda take bayar da agajin farko. Dan kungiyar Annahada zai iya tafiya kowace kasa ta duniya ya yi aikin agaji, ba kamar sauran kungiyoyi ba.

Duk da kun samu shekara goma da kafuwa a kasar nan amma kuma ba kasafai ake jin duriyar ta ba, me ya sanya haka?

Eh! Akwai dalili, shi ne rashin dawowar maulanmu gida da zama Maiduguri, domin kafin nan ya fi zama a kasashen Larabawa. Gudanar da ita daga kasashen waje da yake yi ne ya sanya ba a san ta ba a Najeriya amma yanzu da yake ya dawo gida, in sha Allahu ayyukanta za su sanya wadanda ba su san ta ba su sani. To, wannan dalilin ne ya sanya yadda ta yadu a sauran kasashen Larabawa ba ta yadu ba a nan Najeriya.

Kowace kungiyar addini tana fitowa da manufar yada addini ko kuma bayar da agaji, me ya sanya kungiyarku ba ta fito da salon rika gina asibitoci da makarantu ba domin manufofinta su bambanta da na saura?

Kamar yadda na gaya ma a farko, a takaice yanzu za mu iya cewa a Najeriya wannan kungiya jaririya ce amma ta bangaren bayar da agaji akwai wani sansanin ’yan gudun hijira da aka bude a Abuja, kungiyar Annahada ta Misira ta zo ta kawo taimakon magunguna ga masu gudun hijira. Da ’yan kungiyar na nan Najeriya aka hadu aka yi aikin bayar da kayan ga wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Me kungiyar take yi domin tallafa wa wadanda suka Musulunta a nan Kudanci, aka kore su daga dangi?

Yanzu haka dalilina zuwa Kudanci ke nan, domin ina yin yawo ne ina yada manufofin kungiyar kuma ina duba irin wadannan mutane da suka Musulunta, domin a kawo masu taimako. Yanzu haka ina garin Kalaba, Jihar Kurosriba. Yana daya daga cikin yawace-yawace da nake yi, domin in ga irin wadannan matsaloli saboda idan na koma in rubuta rahoto in aika wa hedkwatar Annahada, in sanar wa shugabaninmu irin matsalolin da Musulmi da ke wurare kaza-da-kaza, domin a taimaka masu.