kungiyar alkalan kotunan gargajiya da shari’a na arewacin kasar nan da manyan alkalai na jihohin Arewa 19 sun gabatar da zaben sabon shugaba na kasa a Jihar Jigawa.
Wadda aka zaba ita ce Hajiya A’isha Sani, a taron da aka yi na kungiyar karo na 40, wanda akan yi a kokarin bunkasa harkokin shari’a a arewacin kasar nan, bisa doron gaskiya, kamar yadda doka ta tanada.
Da take jawabi, shugaban kungiyar, Mai shari’a A’isha Sani Tahir, a yayin da Mai shari’a Aminu Sabo Ringim ya jagoranci tawagarsu domin ganawa da gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a gidan gwamnati, ta ce an sami canjin sabon jagorancin kungiyar, wadda kowa daga cikin ’ya’yanta ke marhabin da zuwansa. Ta ce za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta ciyar da kungiyar gaba.
Mai shari’a A’isha ta nuna jin dadinta game da yadda gwamnatin jihar Jigawa amshi bakuncinsu hannu biyu, ta ba su kulawa ta musamman a taronsu har suka kammala zabensu cikin kwanciyar hankali ba tare da sun fuskanci wata barazana ba.
Ta yaba da gwamnati da matsayin jihar, wadda ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya, kuma ta cancanci jinjina saboda namijin kokarin da ake yi na samar da tsaro a cikinta.
Da yake maida jawabi, Gwamna Lamido ya yaba da yadda aka gudanar da zaben, ya taya ta murnar cin zaben, ya kuma shawarce ta ta rungumi kowa da kowa a tafi tare, ba tare da nuna bambanci ba, wanda yake haifar da rigingimu, ya hana al’amuran kungiya su tafi daidai.
kungiyar Alkalai ta yi sabon shugaba
kungiyar alkalan kotunan gargajiya da shari’a na arewacin kasar nan da manyan alkalai na jihohin Arewa 19 sun gabatar da zaben sabon shugaba na kasa…