✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kungiyar Al-Ihsan Yakasai ta kaddamar da ayyukan cike ramuka a Kano

kungiyar taimakon kai da kai ta Al-Ihsan  Yakasai da ke yankin karamar Hukumar  Bichi ta   kaddamar da aikin  cike manyan ramuka da ke kan…

kungiyar taimakon kai da kai ta Al-Ihsan  Yakasai da ke yankin karamar Hukumar  Bichi ta   kaddamar da aikin  cike manyan ramuka da ke kan hanyar Kano zuwa Katsina domin ganin an rage yawan aukuwar munanan hadrran da ake yi a wannan babbar hanya.

Shugaban kuniyar Malam Auwalu Rabo Yakasai ya shaida wa Aminiya cewa sun yanke shawarar gudanar da wadannan ayyuka ne domin ganin yadda ake rasa rayuka da dukiyoyi sakamakon karo da ake gwabzawa wajen kokarin da masu ababen hawa ke yi na kauce wa ramukan da ke kan wannan titi, inda kuma ya jaddada cewa kungiyar za ta ci gaba da gudanar da wannan aiki duk da cewa suna fama da karancin kayan aiki kamar wulbaro da magirbai na hakan kasa da digogi da tebura.

Sannan ya sanar da cewa kungiyar ta kunshi direbobi da yaran mota, da ke aiki a wannan babban titi, sannan suna kara samun membobi a koda yaushe da ke shiga ba da gudummawa wajen ganin ana cike ramukan da ke zamowa barazana ga ababen hawa. Sannan ya bayyana cewa dukkanin ‘ya’yan  wannan  kungiya suna yi ne domin  taimakon juna kuma sune suke hada dan abin da suke aiki a junan su.

Malam Auwalu Rabo ya gode wa direbobin da ke jigila a wannan titi na Kano zuwa Katsina saboda gudummawar da suke bai wa kungiyar a duk lokacin da suka fito kan hanya domin gudanar da aikin cike ramuka, inda ya ce direbobi suna basu taimako domin ganin sun kara sayen kayan aiki ba tare da jiran sai gwamnati ta yi masu ba.

Kwamandan shiyyar Bichi na Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa wato  FRSC, Alhaji  Mustapha  Alkassim, ya  yaba wa wannan kungiya ta Al-Ihsan Yakasai saboda ayyukan da suke yi ganin yadda wadannan ramuke ke haddasa munanan hadurra a koda yaushe.

Alhaji Mustapha kuma ya ja kunnen direbobi kan su guji yin tukin ganganci musamman ganin yadda wannan hanya ta lalace kuma ga munanan ramuka da ke jawo karo wajen yin aron hannu da ake yi, sannan ya jaddada cewa jami’an sa suna kokari kwarai da gaske wajen fadakar da direbobi dangane da yawan gudu da mugun lodi da kuma rashin kula da lafiyar ababen hawan su.

A na sa bangaren, shugaban kwamitin koli na kungiyoyin ayyukan gayya na Jihar Kano Alhaji Ibrahin Garba Aminu kofar Na’isa ya nuna jin dadin sa ne bisa yadda wannan kungiya ta Al-Ihsan Yakasai ta ke gudanar da wannan aikin, tare da yin kira ga sauran kungiyoyin direbobi da su yi koyi da wannan kungiya wajen yin gyara kan titunan da suke jigila domin rage yawan hadurran da ake samu a kodayaushe.

Haka kuma ya yi musu albishir da cewa kwamitin koli na kungiyoyin ayyuka gayya na Jihar Kano zai sanya wannan kungiya cikin jerin kungiyoyin da za su rika samun kayan aiki a duk lokacin da gwamnatin jihar Kano ta samar da su cikin yardar Allah.