✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta zargi dan Majalisar Kano da amfani da takardun karatu na bogi

Zargin ba shi da tushe bare makama.

Wata kungiya mai suna ‘Gamayyar Matasan Gaya’, ta zargi wani dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Gaya/Ajinji/ Albasu a jam’iyyar APC, Abdullahi Mahmud Gaya, da amfani da takardun shaidar karatu na bogi.

Jaridar Daily Times ta rawaito cewa, Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a karshen makon nan.

Sanarwar ta ce: “A wani lamari mai ban mamaki da al’ajabi, an gano wani dan siyasa a Kano da yin amfani da takardun karatu na bogi.

“Dan siyasar wanda ya rike mukami a gwamnatin jiha, yanzu kuma dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Gaya, Ajingi da Albasu, ya yi ikirarin cewa ya samu takardar shaidar kammala karatun ‘Diploma’ a Jami’ar Abuja.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa bayan binciken da aka yi an gano cewa ba a bi doka ba wajen kammala karatun kuma takardun shaidar karatun sun nuna yadda dan majalisar ya fadi wani kwas ba tare da ya yi gyaransa ba.

Sai kungiyar ta ce ba a san dalilin da hukumar jami’ar ta kawar da kai ta bayar da sakamakon ba tare da bin tsarin da ya dace ba a shekarar 2001.

Kungiyar ta ce wasu gungun ‘yan jarida ne da suka gudanar da bincike kan dan siyasar suka gano hakan, inda suka tuntubi jami’ar da tambayoyi domin tabbatar da sahihancin takardun da ake takaddama a kai.

Sai dai da aka tuntubi mai taimaka wa dan majalisar a bangaren yada labarai, Malam Abba Dukawa, ya ce sam maganar zargin da ake wa dan majalisar ba shi da tushe bare makama, kuma su ba su taba sanin da wata kungiya mai wannan sunan ba.

Sai dai kuma Jaridar ta Daily Times ta ci gaba da cewa binciken ya gano dan majalisar ya mika wa Hukumar Zabe INEC shaidar kammala karatun makarantar firamare wacce ke dauke da sunan wani daban da nasa ba.

Ta dage kan cewa takardun da ya mika a fom dinsa na CF001 wadda ita ce takardar rantsuwa da shaida wadda hukumar zaben take amfani da ita wajen tantance ‘yan takara, an gano cewa a nan ma ya mika takardar shaidar kammala karatun firamare ta bogi mai dauke da sunan Abdullahi Mohd yayin da sauran takardunsa ke dauke da sunan Mahmud Abdullahi Gaya.

Kungiyar ta ce ba ta san dalilin da ya cire takardar shaidar ‘Babbar Difloma’ daga wannan fom din na CF001 da ya cike domin yin takara a Zaben 2023 ba, wadda ya yi amfani da ita a takararsa ta Zaben 2019.

Kungiyar ta ce mutane da yawa sun nuna shakku kan amincin INEC idan har za a iya amfani da wannan kwamacala a kan idonta, wanda kuma ya jefa ayar tambaya game ingancin ilmin da dan siyasar ya yi a baya.

Idan za a iya tunawa, an taba samun makamancin wannan zargin kan, Salisu Buhari, wanda shi ma ya shiga zabe ya kuma yi nasara da jabun takardun karatu kamar yadda zargin ya nuna a wancan lokaci da ya nemi wakilcin Karamar Hukumar Nasarawa ta Jihar Kano a Tarayya.