Wata kungiya da ke tallafa wa marayu da zawarawa a garin Kafanchan ta raba wa marayu da zawarawa kimanin 200 kayan abinci da suka hada da gero da shinkafa da dawa da masara da sukari da atamfa da kuma yadidduka.
A lokacin da yake yi wa Aminiya karin haske a wajen bikin rabon kayayyakin, shugaban kungiyar, Alhaji Muhammad Umar ya ce kungiyarsu ta kwashe akalla shekara 15 tana gudanar da aikace-aikacenta da suka hada da daukar nauyin karatun marayu marasa galihu tun daga firamare zuwa karamar sakandare, sannan sun yi rajista da wani shagon sayar da magunguna inda za a je da yaro idan ba ya da lafiya kan matsalar da ba ta wuce Naira dubu biyu ba. Ya ce dukkan wadannan ayyuka da suke yi suna gudanar da su ne da taimakon da suke samu daga daidaikun jama’a.
A karshe ya yi kira ga masu hali da su rika ware wani abu a cikin dukiyar da Allah Ya ba su don tunawa da kananan yaran da suka rasa iyayensu da kuma matan da suka rasa mazansu kuma ba su da wani karfi.