Kungiyar Generation For Peace da ke kokarin wanzar da zaman lafiya ta hanyar ilimantar da mutane musamman matasa muhimmancin son juna da fahimtar juna ta shirya taron bita kan zaman lafiya a Kaduna.
kungiyar wadda ke samun tallafi daga Robert Bosch Stiftung, ta fara aikace-aikacenta ne a watan Fabrairun bara, inda take shirya taro ga matasa sau biyu a duk wata da nufin koyar da matasan hanyoyin zaman lafiya da fahimtar juna da girmama juna.
A wannan taro da kungiyar ta shirya wanda aka fara tun farkon watan Maris da muke ciki, an tattauna a kan muhimman abubuwan da suke janyo rikici da hanyoyin da za a magance su. Mahalarta taron sun koyi hanyoyin rungumar juna ta hanyar girmama addinan juna da barin nuna bambancin kabilanci da kuma yada labaran karya wadanda ka iya tunzura mutane su fara kashe juna.
An gudanar da taron bitar ne a unguwanni takwas da suka hada da Hayin Banki a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa inda aka tattauna a kan illar yada labaran karya, sai Unguwar Kawo, ita ma a karamar Hukumar Kaduna ta Arewa inda aka tattauna a kan illar amfani da miyagun kwayoyi wanda shi ma ke taimakwa wajen sanya matasa su yi barna ba tare da sun sani ba.
Sai kuma karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, inda aka gudanar da taro a Unguwar Makera kuma aka tattauna a kan matsalar rikicin siyasa. Sai kuma karamar Hukumar Igabi, inda aka gudanar da taron a garin Rigasa kuma aka tattauna a kan illar zaman kashe wando sai kuma a karamar Hukumar Chikun inda aka gudanar da taron bitar a garin Telebision da Unguwar Romi kuma aka tattauna a kan illar amfani da miyagun kwayoyi da kuma rashin jituwa tsakanin mutane wanda ke canjawa ya koma rikicin kabilanci da addini.
Wadansu daga cikin wadanda suka halarci taron bitar sun nuna farin cikinsu kan yadda suka halarci irin wannan taron bitar, inda suka ce wannan ne karo na farko da suka samu irin wannan damar, sannan sun yi alkawarin za su yi amfani da abin da suka koya wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Nura Hassan daga Kawo cewa ya yi, “Taron nan ya taimaka min wajen samun damar zantawa da masu ruwa- da-tsaki a harkar tsaro. Zan iya cewa gaskiya kungiyar Generation for Peace tana bayar da dama ga matasa su shiga harkar samar da tsaro a Kaduna.”
Shi kuma John Jerry cewa ya yi, “Bisa irin wannan horo da muka samu, ina fata wata rana zan samu makwabci Musulmi a Unguwar Romi.”
Shugaban Tsare-Tsare na kungiyar Eric John, ya ce za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da zaman lafiya da son juna a Jihar Kaduna tare da fadada ayyukan kungiyar.