Kungiyar Ci gaban Arewa mai suna Arewarmu Duniyarmu ta karrama sarakunan biyu masu daraja ta daya da wadansu fitattun mutane daga Arewa maso Gabas bisa kwazonsu wajen ciyar da al’umma gaba.
Da yake jawabi a wajen karramawar Shugaban Kungiyar ta Kasa, Alhaji Ibrahim Haruna Tukulma, ya ce an kafa kungiyar ce domin ci gaban Arewa baki daya sannan tana da reshe a Jihar Legas; kuma suna shirin bude wani reshe a Fatakawal nan gaba.
Ya ce sun kafa kungiyar ce domin ganin sun hada kan duk wani dan Arewa, duk inda yake a kasar nan domin duk abin da zai faru ya zama akwai wanda zai yi magana da yawun ’yan Arewa.
Ya ce kungiyar ba ta siyasa ko ta addini ko ta gwamnati ba ce. A’a kungiya ce don ci gaban ’yan Arewa gaba daya wacce aka kafa ta a ranar 28 ga Oktoban shekarar 2017 a Mogadishu a Kaduna.
A jawabi Shugaban Taron, Alhaji Habu Mu’azu, cewa ya yi kafa wannan kungiya ta Arewarmu Duniyarmu ya yi daidai da yadda ake son a yi koyi da kyawawan halayen su marigayi Abubakar Tafawa Balewa da Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.
Alhaji Habu Mu’azu ya kirayi ’yan Arewa musamman matasa su yi koyi da halin wadancan shugabani da suka gabata domin matasan su ne abin koyi nan gaba.
Turakin Herwagana, Alhaji Musa Muhammad Gidado, wanda shi ne jagoran kungiyar a Arewa maso Gabas ya ce kungiyar tana da manufofi masu kyau daga ciki akwai shawo kan matasa daga harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi da gyaran tarbiyyar wadanda suka kangare.
Ya roki gwamnati ta samar musu da fili da za su gina cibiyar horar da matasan sana’o’i domin ba yadda za a yi a gyara tarbiyyar matasa ba tare da aikin yi ba.
Da yake jawabin maraba, Yeriman Gombe, Babban Hakimin Garin Gombe da Kewaye Alhaji Abdulkadir Abubakar, yaba kyawawan manufofin kungiyar ya yi inda ya ce a matsayinsa na Uban Kungiyoyi a Jihar Gombe ya kula ayyukan kungiyar sun sha bamban da na sauran.
Daga nan sai ya taya sarakuna da sauran wadanda aka karrama murnar wannan lambar yabo da aka ba su bisa jajircewarsu wajen taimakon al’umma.
Da yake jawabi godiya a madadin wadanda aka karrama, Mai martaba Sarkin Yamaltu Alhaji Abubakar Aliyu, ya ce abin da ya burge shi da kungiyar shi ne yadda ta himmatu wajen hada kan ’yan Arewa da kuma gudanar da ayyukan madalla da take yi.
Sarkin Yamaltu, ya jinjina wa matasa kan yadda suka halarci taron suka ji da kunnensu irin burin da ake da shi a kansu na su zama mutanen kirki.
A lokacin taron an bada lambar yabon ga sabon Sarkin Gona Alhaji Umar Bappah Abdulkadir Abdulsalam da sabon Sarkin Yamaltu Abubakar Aliyu da Hajiya Maryam Garba Bagel daga Jihar Bauchi da tsohon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano Muhammad Wakili da Kocin ’Yan Kwallon Najeriya ’yan kasa da shekara 17 (U-17), Manu Garba da sauransu.