kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Makamantarts (SSAEAC), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da binciken kwarewa a duk kamfanonin samar da wutan lantarki domin tabbatar da cewa kamfanonin suna aiki yadda ya kamata.
kungiyar ta ce, binciken kwararrun yana da matukar amfani musamman domin a san yanayin karfin kowane kamfani da darajarsa a lokacin da aka karbi ragamar samar da wutar da kuma darajar kamfanin a yanzu.
Shugaban kungiyar, Kwamared Chris Okonkwo wanda ya fadi haka a wata sanarwa ya ce “Ya kamata gwamnati ta gano ko an samu karin karfi kuma wace daraja asuke da ita da kuma a san ko an karkace daga alkawarin da aka yi kafin watan Oktoban shekarar 2013 zuwa yau da kuma sanin karfinsu a kowane lokaci, domin babbu tabbas kan kamfanonin..
kungiya ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta binciki kamfanonin wutar lantarki
kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Makamantarts (SSAEAC), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da binciken kwarewa a duk kamfanonin samar da wutan lantarki domin…