✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kuncin Rayuwa: Yadda Trust Radio Ya Faranta Ran Masoya a Abuja

Mutane da dama – maza da mata, manya da kanana, daga ciki da wajen Abuja – ne suka kasance a rumfar Trust Radio a dandalin.

Bisa al’ada, duk ranar 14 ga watan Fabrairu, wuraren shakatawa na birnin Abuja kan cika da mutane suna farin cikin zagayowar Ranar Masoya.

Amma a bana, mutanen da suka ziyarci dandalin Millenium Park sun bayyana cewa ranar ta zo musu a hagunce saboda matsin rayuwar da suke fuskanta.

Sai dai kuma, a karshe sun tafi da farin ciki bayan haduwarsu da ma’aikatan Trust Radio, wadanda suka je dandalin don taya masoya murnar wannan rana.

Mutane da dama – maza da mata, manya da kanana, daga ciki da wajen Abuja – ne suka kasance a rumfar Trust Radio a dandalin.

Mutanen sun nuna matukar farin ciki sannan suka yi godiya ga Trust Radio saboda shirya wannan taro da suka bayyana da cewar shi ne irinsa na farko da suka gani a tsawon lokacin da suke ziyartar dandalin na Millennium Park.

Wasu da muka samu zantawa da su daga mahalarta dandalin (hirar da muka yada kai-tsaye ta shafinmu na trustradio.com.ng sun bayyana farin ciki da yabo ga Trust Radio.

Daya daga cikinsu, Nana Firdausi, cewa ta yi, “E, gaskiya ina jin labarin Trust Radio Abuja… yau ga shi na hadu da ku, Allah Ya kara muku daukaka Ya sa a ji ku a ko’ina a fadin duniya”.

”Na fi jin dadin bikin Ranar Masoya na wannan shekarar saboda yadda Trust Radio ta shiryar mana wannan taron mai kayatarwa”, inji Ummussalma Muhammad.

“Nishadin taron ma har ya sa na manta yanayin da ake ciki na matsin tattalin arziki wanda ya rage armashin bikin Ranar Masoya na bana saboda kuncin rayuwar da muke ciki”, a cewar Lubna Ishaq.

Wani bangare na bikin shi ne raba kyaututtuka ga masoyan da suka kasance a dandalin, ko da kuwa ba tare da masoyansu suka je wurin ba.

Nana Fadima na cikin wadanda suka yi nasarar cin kyaututtukan da muka sa a gasar masoya da muka yi wa take da “Gasar Ranar Masoya”; bayan ta bude jakar da muka ba ta mai dauke da kayayyaki daban-daban cewa ta yi: “Ma sha Allah, Trust Radio, na ga jotter ta rubutu, da biro, da ‘key holder’, ga kuma babbar jaka duka masu ɗauke da tambarinku da sunanku.

“Gaskiya Trust Radio na gode, Allah Ya sa ku fi haka kuma a ji ku a ko’ina”.

Bikin, wanda aka fara shi da ƙarfe uku na ranar Laraba 14 ga watan Fabrairun 2024, ya kammala lami lafiya kuma kusan dukkan wadanda suka halarta sun samu kyaututtuka masu ɗauke da tambari da sunan Trust Radio 92.7.

Kyaututtukan sun hada da masakin ’yan makulli (key holder) ko biro, ko littafin rubutu, da jakunkuna.

Trust Radio dai, gidan rediyo ne a Abuja mai taken “Amintacciyar Muryarku” wanda bangare ne na kamfanin Media Trust, mamallakin jaridun Daily Trust da Aminiya da kuma gidan talabijin na Trust TV.

A yanzu haka yana watsa shirye-shiryensa ta intanet a trustradio.com.ng da kuma ta shafukan sada zumunta da muhawara wato, Facebook da X (Twitter a da) da Instagram da TikTok duka a @trustradiolive.