✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kuncin da mutanen Kaduna ke fuskanta ya dame ni — El-Rufai

Yanayin tsaron jihar abu ne mai tada hankali matuka.

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya ce yana cike da damuwa a kan halin kunci da matsalar tsaro ta haifar a jihar.

El-Rufai ya yi furucin hakan ne a yayin da yake karbar rahoto dangane da tsaron jihar a rubu’i na biyu na bana.

A cewarsa, kididdigar bayanan kan yanayin tsaron jihar abu ne mai tada hankali matuka duba da yadda matsalar tsaron ta ta’azzara.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jahohin da ’yan bindiga suka matsawa inda dalilin haka daruruwan mazauna garin na hannun ya dindigan ko sun rasa ransu.

Alkaliman na nuni da cewa yanayi na tsaro a jihar a rubi’u na biyu na wannan shekarar ta 2021 ya tabbatar da halin ni ’yasu da a ’yan jihar ke ciki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, rahoton ya kuma zayyana irin fad-tashin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi wajen shawo kan lamarin.

Har ila yau, gwamnan ya kara da cewa sakamakon binciken ya nuna kwalliyar tana biyan kudin sabulu a kan kokarin da gwamnati keye wajen dakile matsalar rashin tsaron.

Ya kara da cewa gwamnatinsa tana nan kan bakanta na jajircewa wajen taimakawa jami’an tsaro, kuma yana kara neman dauki da tallafi daga Gwamnatin Tarayya domin magance matsalar baki daya.

Ya bukaci mazauna jihar da da su zama masu bin doka da oda sannan su tabbatar sun zama jakadu na zaman lafiya a jihar.

Ya kara da cewa mazauna karkara da dagatai na Zangon Kataf da kuma Karamar Hukumar Jema’a da kada su gaji wajen yada sakon zaman lafiya da junan.

Sannan ya jajanta wa mutanen da rashin tsaro ta shafa da kuma jami’an tsaron da suka rasa rayukansu a sanadiyyar rashin tsaron.

“Ina baku tabbaci muna yin duk wata mai yiwuwa don ganin kowa ya zauna cikin aminci da lumana kuma kawar da wannan matsalar shi ne nauyi na farko da rataya a wuyanmu,” a cewar gwamnan.