✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din Azam na Tanzaniya ya fara zawarcin Keshi

Kulob din Azam wanda shi ne zakara a gasar rukuni-rukuni na kasar Tanzaniya ya bayyana cewa ya fara hankoron ganin ya dauke tsohon Kocin Najeriya…

Kulob din Azam wanda shi ne zakara a gasar rukuni-rukuni na kasar Tanzaniya ya bayyana cewa ya fara hankoron ganin ya dauke tsohon Kocin Najeriya Super Eagles Stephen Keshi.

Kulob din ya ce Keshi yana daga cikin jerin ’yan kwallon da ya gayyata don ya zabi daya daga cikinsu.
Kulob din ya kori tsohon kocinsa ne dan kasar Kamaru mai suna Joseph Omog a ranar Litinin da ta wuce, bayan kulob din El-Mereikh na Sudan ya fitar da shi a gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Afirka (Champions League) da ci 3-2.
A wasan farko da aka yi a Tanzaniya, Azam ne ya doke na El-Mereikh da ci 2-0 amma abin mamaki a wasa zagaye na biyu sai El-Mereikh na Sudan ya yi biji-biji da na Azam da ci 3-0 al’amarin da ya sa aka yi waje rod da kulob din Azam a gasar.
Hakan ta sa kulob din ya bayar da sanarwar sallamar tsohon kocinsa Joseph Omog da mataimakinsa Ibrahim Shikanda kuma yake neman maye gurbinsu da sabon koci.
Sakatare-Janar na kulob din Azam Idrissa Nassoro ya tabbatar da cewa tuni kulob din ya gayyaci masu horarwa ciki har da Keshi don tantance wanda zai gaji kocin da suka kora nan ba da jimawa ba.