✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kulob din Atletico Madrid ya shiga rudu

A ranar Litinin da ta wuce ne kulob din billareal ya lallasa na Atletico Madrid da ci 3-0 a gasar La-Liga ta Sifen da hakan…

A ranar Litinin da ta wuce ne kulob din billareal ya lallasa na Atletico Madrid da ci 3-0 a gasar La-Liga ta Sifen da hakan ta sa kulob din ya shiga rudani.

Kawo yanzu kulob din Real Madrid da ke saman teburin gasar ya ba na Atletico Madrid tazarar maki 12 kuma wannan shi ne kakar wasa mafi muni tun bayan da kocin kulob din Deigo Simeino ya karbi ragamar horar da kulob din.
“Wannan ita ce kakar wasa mafi muni ga kulob din a tsakanin shekaru biyar da suka wuce,” inji Kyaftin Gabi a wata hira da tashar rediyo ta Cadena Ser ta Sifen ta yi da shi.
Atletico Madrid ta samu rashin nasara 4 a cikin wasanni bakwai da ta yi a gasar La-Liga a ’yan kwanakin nan.