Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Birgediya Buba Marwa (Mai ritaya) ya ce kusan kullum sai an yi masa barazanar kashewa.
Buba Marwa ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida bayan ganawarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
“Kusan kullum sai an yi min barazar kisa saboda kowa na iya kiran wayata; Ana kuma turo min irin wadannan sakonni ta hannun abokan aikina, wani lokaci kuma mutanen da ba mu sani ba, amma inan nan kan bakata. Sai dai kuma ina yin taka-tsantsan,” inji shi.
Buba Marwa, ya ce barazanar da ake masa ba za ta sa ya daina aikinsa ba, ya kuma bayyana damuwarsa cewa matsalar ta’ammali da miyagun kwayoyi ta shiga makarantun firamare.
Shugaban na NDLEA ya ce ya ziyarci Fadar Shugaban Kasa ne domin yin bayani ga Shugaba Muhammadu Buhari kan aikace-aikacen hukumar na baya-baya nan.
A cewarsa, daya daga cikin manyan ayyukan hukumar na baya-bayan nan shi ne batun gina wa jami’an hukumar barikoki, kuma suna ganin haske daga Shugaban Kasar.
Shugaban na NDLEA ya ce sun kuma tattauna da Shugaba Buhari a kan batun daukar sabbin ma’aikata, duba da girman aikin da ke gaban hukumar da kuma rashin wadatattun ma’aikatanta da ke addabar ta.
Marwa, bayanna cewa hukumar ta fara wayar da kai a makarantu game da illolin ta’ammali da miyagun kwayoyi, tun da har a makarantun firamare ana samun yara masu amfani da su.