✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

kulafucin iyaye ga ’ya’ya! (2)

Ke nan daga abin da muka tattauna a baya ya dace, kila ma a ce ya zama dole mutane mu mayar da tunaninmu waje daya…

Ke nan daga abin da muka tattauna a baya ya dace, kila ma a ce ya zama dole mutane mu mayar da tunaninmu waje daya dangane da yadda muke dubar ’ya’yan da muke cin karo da su a tsarin rayuwa ta yau da kullum. Yaya muke ji a lokacin da muna tafiya cikin mota ko a kasa ko kuma kan babur ko keke muka yi kicibis da yaro na bara, ba abin da yake bukata sai mu ba shi daga abin da muke da shi, ya samu na cin abinci? Yaya muke ji a lokacin da muka kalli yaron nan yana rokonmu cikin tsummokara, idanu duk kwantsa, ba takalmi, kuma duka bai wuce dan shekara 6 zuwa 11 da haihuwa ba, ga shi yana fuskantar kalubalen rayuwa, tun bai san inda kansa ke masa ciwo ba? Yaya muke ji a lokacin da muka tuna cewa muna da kamarsa a gida, amma shi namu dan yana cikin kwanciyar hankali da jin dadi, a wannan lokaci ma kila yana can yana karatu a daya daga cikin kyawawan makarantun da ke a cikin wannan kasa ko kasashen waje? Shin mun taba kawowa a cikin ranmu cewa wadannan ’ya’yan da muke faman bautar da su a matsayin almajirai ’ya’yan wasu ne kamar namu ’ya’yan? Mun taba tunanin cewa ba wata rawa ce muka yi ba Allah Ya kebe namu ’ya’yan daga fadawa cikin irin wannan tarkon? Shin yaya muke ji a lokacin da muka kwashi yarinyar nan muka kai ta cikin gidajenmu, muna bautar da ita a matsayin ’yar aiki, saboda kawai iyayenta da ita kanta suna sanye da rigunan talauci da rashi da kuncin rayuwa? Yaya muke ji idan muka gan ta cikin damuwa da rashin walwala da aiki tamkar injin a cikin gidan, alhali ga namu ’ya’yan nan cikin gida tsararrakinta, suna wasa da walwala da jin dadi, amma muna bautar da ’ya’yan wasu? Muna jin cewa don Allah Ya tarfa wa garinmu nono, ita waccan da muke bautar da ita Allah bai tarfa wa nata ko na iyayenta ba, shi ke nan sai mu kasance azzalumai? Shin muna jin namu ’ya’yan sun hau tudun-mun-tsira ne don suna cikin daula yanzu?

Idan muna ganin hotonmu ko na abokinmu ko muna ganin surarmu ko ta wani kusa da mu daga wannan bayani mene ne mafita? Mu tausaya musu ne kurum? Me muke rayawa a cikin rayukanmu na kawo karshen wannan hali da ’ya’yan wasu ke ciki, a matsayinmu na talakan kasa ko mai kudi ko mulki ko kuma mai fada a ji?
Ba wannan kadai ba, a cikin unguwarmu, yaya muke kallon ’ya’yan wasu, a matsayin ’ya’yanku ko kuwa? Muna daga cikin masu korar ’ya’yan makwabta daga cikin gidanmu don wai muna tunanin cewa, sun zo su ci abincin gidanmu tare da namu ’ya’yan? Ko kuwa muna cikin masu korar ’ya’yan wasu daga gidajenmu don wai kada su bata mana tarbiyyar namu ’yayan? Muna ganin yin haka shi ne mafi alheri? Shin mayar da ’ya’yan wasu ’ya’yan wasu kurum, ba namu ba ne, me yake jawo wa al’umma? Shin ’ya’yan nan da ba namu ba da ke gararamba bisa titi duk ranar Allah muna ganin za su rayu da mutuwa cikin wannan hali ne har abada? Shin ba mu tunanin cewa in mu ne yau ba mu ne gobe ba? Me zai hana ke nan mu dauki kowane yaro a matsayin da; mu suturta shi, mu kyautata rayuwarsa, mu inganta rayuwarsa, mu tabbata ya samu muhalli da abinci da abin sha da kiwon lafiya da tsaro da duk wata kulawa da ta dace da shi? Me zai hana mu yi amfani da matsayi ko iko ko isa ko daukaka da Ubangiji Ya yi mana mu rage wa irin iyayen wadannan yara da ke cikin irin wannan radadin talauci da yunwa da damuwa da kuma kunci da suke ciki, mu ga in ba za mu rage radadin fashi da makami da wasu miyagun ayyukan assha da ke faruwa a cikin kasa ba? Me zai hana mu yi amfani da karfin gwamnati da muke da shi mu ga mun rage wannan badakala da ke mana barazana a rayuwa a kullum rana ta Allah? Mu tuna, kin yin haka da sani ko da ganganci ko kuma cikin jahilci zai biyo mana baya ne da nasa matsaloli!
Kamar yaya? Irin wannan ba abin da yake jawo wa illa rarraba kai da nuna bambanci da kishi da kyashi da rashin kaunar juna da kuma gaba da tashin hankali, ba wai kuma a tsakanin al’umma ta kusa kurum ba, har da sauran sassan kasa baki daya. Domin ta haka ne yara ke tashi da kyamar juna da nuna isa da kuma rarrabuwa, a wajen mulki ne ko tsarin kasuwanci ko kuma zamantakewar yau da kullum, musamman idan aka yi la’akari da irin yadda fashi da makami da miyagun ayyuka ke kara gudana a tsakanin jama’a. kila idan muka yi nazarin yadda muke dubar ’ya’yanmu ba tare da dubar na wasu ba, duk kuma abin da ya same su bai dame mu ba, a iya samun amsar wasu daga cikin amsoshin matsalolin rayuwarmu a yau, domin maganin irin ta a gobe.

Mun kammala