Kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci Shugaban Darikar Katolika reshen Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah ya ajiye mukaminsa na Sakatare Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa (NPC).
MURIC ta yi kiran ne bayan sakon Kirsimetin Bishop Kukah, wanda a ciki ya ce Najeriya na dab da durkushewa a karkashin Shugaba Buhari.
- An gurfanar da Matashi saboda cizon Budurwarsa a Mama
- Za mu yaki hauhawar farashin kayan abinci a 2021 — Buhari
- Yadda Buhari zai sa hannu kan kasafin 2021
- Bom ya kashe mafarauta 7 a Borno
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, a cikin wata sanarwa ya ce kalaman na Bishop Kukah ba su dace su fito daga mutum kamarsa mai mukamin Sakataren NPC wanda tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar ke jagornta ba.
“Kukah ya sauka daga mukaminsa na Kwamitin Zaman Lafiya cikin mutunci saboda rashin yin hakan zai yi illa ga kimar kwamitin.
“Rashin saukarsa zai nuna cewa manufar kafa Kwamitin shi ne domin ta zama ta ko-a-mutun siyasa,” inji Darakan na MURIC.
Sanarwar ta ce saukar Bishop Kukah daga mukamin na NPC shi ne abin da ya dace saboda zargin da ake masa a matsayin jami’in kwamitin.
Farfesa Akintola ya ce NPC na bukatar samun karbuwa daga dukkanin bangarorin al’umma domin ya samu gudar da aikinsa yadda ya kamata.
Muna bayan Kukah —PFN
Said dai kuma Kungiyar Mabiya Darikar Pentecostal ta Najeriya (PFN) ta goyi bayan Bishop Kukah wanda ta ce gaskiya yake fada, don haka kar a takuwa masa.
Shugaban PFN, Felix Omobude ne ya bayyana haka tare kira da a daina sukar Sakataren na NPC.
“Gaskiya ya gaya wa gwamnati kuma abin da ke zukatan yawancin ’yan Najeriya ke nan. Shi ba makiyin gwamnati ba ne, gaskiya yake so kuma ina goyon bayanshi dari bisa dari,” inji shi.
Shi ma mai fafutikar samar da adalci da zaman lafiya, Rabaran, Gideon Para-Mallam, ya yi kira ga Fadar Shugaban Kasa ta saurari kiran da ya ce Bishop Kukah ya yi ne da muryar miliyoyin Kiristoci da Musulmin Najeriya daga dukkannin yankunan kasar.
Para-Mallam ya ce ya kamata kiran ya zama dalilin da gwamnati za ta yi karatun ta-nutsu wurin tunkarar matsalolin kasar ba biye wa “dadin bakin ’yan fadarta ba.”